ƘUNGIYAR masu gidajen kallo a Jihar Kano ta bayyana cewa a yanzu ba ta ƙarƙashin kulawar Hukumar Tace Finafinan ta jihar, don haka kada wani ɗan ƙungiya ya biya kuɗaɗen da hukumar ke cewa su bayar.
Hakan ya fito ne a wani taro da ƙungiyar ta shirya wa ‘ya’yan ta a yau Litinin a gidan kallo na Lahai da ke Titin Abdullahi Bayero a garin Kano.
Shugaban ƙungiyar, Sharu Rabi’u Ahlan, ya ce sabuwar dokar Hukumar Buɗe Ido Da Yawon Shaƙatawa ta Jihar Kano ta ambaci gidajen kallon ƙarara, wato ‘viewing centres’, a cikin kulawar ta, wanda hakan ya nuna cewa gidajen kallon sun bar kulawar Hukumar Tace Finafinai.
Sharu ya ƙara da cewa daga yanzu duk masu gidajen kallo za su maida lamarin su ne zuwa waccan hukuma, kuma hakan wata dama ce da za ta ƙara inganta al’amura da samun daidaito a sana’ar su.

Da ya ke ƙarin bayani dangane da wani saƙo da Hukumar Tace Finafinai ke aika wa masu gidajen kallo ina ta umarce su da su biya wasu kuɗaɗe, Sharu Rabi’u ya ce wa ‘yan ƙungiyar su dakata kada su biya har sai abin da ƙungiya ta umarce su.
Haka zalika, ya yaba da irin goyon bayan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke ba ƙungiyar tasu.
Ya ce ya zama wajibi ƙungiyar ta yaba wa gwamnati tare jaddada bin dokokin gwamnati, musamman wannan sabuwar doka da ta ɗauke su daga ƙarƙashin Hukumar Tace Finafinai.
Taron ya samu halartar masu gidajen kallo da dama daga sassa daban-daban na jihar.