• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Lamaj: Zan koma finafinan Turanci tunda kasuwar na Hausa ta durƙushe

by DAGA ABBA MUHAMMAD
August 23, 2020
in Tattaunawa
0
Hajiya Fatima Ibrahim (Lamaj), shugabar MOPPAN ta Jihar Kaduna

Hajiya Fatima Ibrahim (Lamaj), shugabar MOPPAN ta Jihar Kaduna

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
SHUGABAR Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwararru masu shirya finafinan Hausa ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, Hajiya Fatima Ibrahim (Lamaj), furodusa ce wadda ba ta gajiya da yin ayyukan shirya finafinai. A Jihar Kaduna dai, babu kamar ta. Ta kan shirya fim uku, huɗu ko fiye da haka a duk shekara.
 
Sai dai a bana an ji ta shiru, kamar babu ita ma a masana’antar. Ba a jin ɗuriyar ta ko kaɗan. Shin me ya faru?
 
Wannan ya sa wakilan mujallar Fim su ka shiga neman ta don jin abin da ya sa aka ji ta kamar an yi ruwa an ɗauke. Wakilin mu ya kuwa sa’ar tattaunawa da ita, inda ta yi masa bayanin abin da ya sa aka ji ta shiru game da aikin shirya finafinai da kuma sauran bayanai game da ita.
 
 
FIM: Hajiya, ki na ɗaya da daga cikin furodusoshin da a Jihar Kaduna ki ke shiga aikin shirya fim a kai a kai, sai kuma aka ji ki shiru yanzu. Ko menene dalili?
 
FATIMA LAMAJ: Abba, in ka duba harkar fim ta duniya baki ɗaya ba motsi ta ke yi ba, in ba hanyar YouTube za ka saida fim ɗin ka ba to ba kasuwa. Da, gidajen talbijin mu ke kai finafinai, yanzu ko an rincaɓe gidajen talbijin da ƙananan finafinan da ba su da tasiri.
 
Sai ka ga mutum ya nemi kuɗin sa, ɗan dubu ɗari ɗaya, dubu ɗari biyu, ya ce zai yi fim. Babu lokeshin mai kyau, babu labari mai kyau, babu hotuna masu kyau, a haka za a je a kai wa gidan talbijin. To, irin waɗannan finafinan ne su ka yi yawa a gidan talbijin, su ne su ka hana gidajen talbijin sayen finafinan mutane. 
 
Amma ka ga YouTube channel, akwai wani channel da na ke yi masu supplying finafinai a Legas, a da za ka ga sun sayi fim da daraja, amma yanzu ya na faɗa min cewa fim ɗin Hausa ba kuɗi mu ke kashewa ba, don haka ya za a yi su rinƙa sayen fim ɗin mu da tsada Sai ya ke ba ni shawara, ya ce da fim ɗin Turanci zan yi, akwai abin da su ke kira ‘share formula’ na YouTube: za a saka ne a YouTube ɗin su, domin babu YouTube ɗin da ya kai nasu samun kuɗi a Afrika baki ɗaya. Ya ce in na yi fim na Turanci na ba shi, duk abin da aka samu ina da kashi sittin ya na da arba’in. 
 
Ka ga ya nuna min a fim ɗin Turanci ake samu. Saboda haka yanzu haka ina shirin shiga aiki, amma fim ɗin “Turanci da Hausa” zan yi – fim ɗin Hausa, amma a Turance, tunda inda kuɗi su ke nan za ka je. 
 
Yanzu ba na tsammanin ko a Ƙofar Wambai za ka samu inda za ka saida fim! Wannan ya sa na ɗan jinkirta wurin aikin fim. Amma ko yanzu da ka kira ni  harkar fim ne ya fito da ni.
 
FIM: A matsayin ku na shugabanni a masana’antar, wane ƙoƙari ku ke yi don ganin kun shawo kan matsalar da masana’antar ta samu kan ta a ciki?
 
LAMAJ: Alhamdu lillah! Ka san yanzu ana cikin wannan annoba ta korona bairos, ba a son cinkoso. Don haka babu yadda za a yi ka fita yin aikin fim da zai tara jama’a. In har kuma ka na so ka shirya fim ɗin da zai karɓu a yanzu, sai dai ka shirya fim a kan masarautu ko kuma ‘epic’. Saboda haka ya sa mu ka sassauta har nan da  zuwa watan gobe; in-sha Allahu za mu dawo da martabar duniyar masana’antar mu. 
 
Kuma na yi magana da shugaban mu (MOPPAN) na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, a kan komai ya tsaya cak, na ce ko da ‘workshop’ a samu a shirya wa mutane, don a fahimtar da su hanyar da za su gudanar da sana’ar su. Ya ce ya na shiri a kan haka, kuma in-sha Allahu za a yi.
 
Lamaj ta ce ba ta yarda da shirya fim mara inganci ba
 
FIM: A lokacin da wannan annoba ta korona bairos ta ɓulla, an dakatar da komai a duniya, har da harkar fim. Ya ku ka ci gaba da gudanar da rayuwa, musamman ganin an shiga wani irin hali?
 
LAMAJ: Abba, ka san mu Musulmai mun yarda da ƙaddara, mun san dukkan abin da ya faru daga Allah ne. Don haka mun yi haƙuri mu ga abin da Allah zai yi mana. Ɗan abin da mu ka tara shi mu ke ci. Amma in-sha Allah, kamar yadda na faɗa maka, komai zai warware.
 
FIM: Wane shiri ku ke yi na shiga tsarin kai finafinan ku Netflix, ganin takwarorin  mu na Kudu sun shiga wannan tsari ana kallon finafinan su a wannan kafar? Yaushe za ku kai wannan matakin?
 
LAMAJ: In-sha Allahu mu na tunanin haka. Akwai wani guruf a WhatsApp na ‘yan Nollywood, kwanan nan ma na sa ‘yan Kannywood a ciki, amma sai ka na jin Turanci za a saka ka, tunda ba da Hausa ake magana ba. Akwai mutane da na san sun yi karatu kuma su na jin Turanci, kuma duk na sa su a ciki. In Allah ya yarda mu ma mu nan a kan hanyar shiga tsarin Netflix. Abin da ake nema, labari mai kyau, hoto mai inganci, ingantaccen sauti, kuma ka samu daraktan da ya san aikin sa.
 
FIM: Idan mu ka koma ɓangaren shugabanci, musamman a Jihar Kaduna, a kwanan baya an yi ta dambarwar cewa an dakatar da ke daga shugabancin MOPPAN reshen Jihar Kaduna. Yaya ake ciki game da wannan batu?
 
LAMAJ: Batun dakatar da ni ai bai taso ba, domin waɗanda su ka ce sun dakatar da ni sun samu ‘wrong impression’ ne a kai na, saboda ina ganin su kan su ba su san me su ke yi ba, don ba zai yiwu a ce zaɓaɓɓiyar shugaba a ce an dakatar da ita ba tare da wani ƙwaƙƙwarar hujja ba, kuma aka ce ba zan je in yi zaɓen shugaba na ƙasa ba, za su tura nasu wakilan. Ni kuma sai na tura mutanen da za su wakilce ni a wurin zaɓen, kuma mutanen da na tura su su ka yi zaɓen. Ka ga ‘automatically’ mitin ɗin da su ka yi a kan sun cire ni bai yi masu tasiri ba!
 
Kuma ban da shugabancin MOPPAN da na ke yi akwai ƙungiyoyi biyu da na ke  yi. Akwai ƙungiyar Kannywood Women Association, ni ce mataimakiyar shugaba; akwai kuma ƙungiyar mata kuma wadda A’isha Halilu ta ke shugabanta, a nan ma ni ce mataimakiya. Ka ga in an cire ni a shugabancin MOPPAN akwai matsala. 
 
Abin da na sani, ni ce shugabar MOPPAN, kuma ni ke gudanar da  harkokin MOPPAN.
 
FIM: Akwai wani cigaba da ku ka samar tun bayan zaɓen ku da aka yi?
 
LAMAJ: Ba zan ce babu ba, tunda akwai mutanen da  a ɓangaren aikin su za a aiko a ce ana buƙatar mai kyamara a wani gidan talbijin, akwai mutanen da su ke aiki a gidajen talbijin; duk ta dalilin MOPPAN su ka samu aikin. Ka ga wannan ma cigaba ne. Akwai wani yaro ma da mu ka sama wa aiki a Tozali TV, shi ne editan su, ni na kai shi da haɗin gwiwar Al-Amin Ciroma.
 
FIM: Akwai wani shiri da ki ke yi game da sauran ƙngiyoyi, kamar su ƙungiyar daraktoci, furodusoshi, jarumai da sauran su?
 
LAMAJ: Gaskiya akwai, amma ba zan yi magana yanzu ba; sai na aiwatar da abin da na ke so, lokacin zan kira ka mu yi hira a kai.
 
FIM: A ƙarshe, wace shawara ki ke da ita ga ‘yan masana’antar Kannywood baki ɗaya?
 
LAMAJ: Abin da zan ce shi ne, ‘yan’uwa na ‘yan Kannywood mu yi haƙuri mu bi dokokin da gwamnati ta kafa, domin mu kare kan mu baki ɗaya (daga COVID-19). Kar mu yaɗa wannan cuta ta korona bairos.

Loading

Previous Post

Yadda mahaifiyar mu ta yi rasuwar bazata – Nasiru Horo

Next Post

Matsala ta da manema aure na – Shalele Umar

Related Posts

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 
Tattaunawa

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 

March 1, 2025
Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah
Tattaunawa

Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah

November 13, 2024
Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala
Tattaunawa

Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala

August 2, 2024
Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde
Tattaunawa

Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde

March 13, 2024
Mahaifiyar Afakallahu ta kwanta dama
Tattaunawa

Afakallahu: Abin da mahaifiyar mu ta karantar da mu

March 11, 2024
Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV
Tattaunawa

Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV

February 14, 2024
Next Post
Jaruma kuma mawaƙiya Rahama Umar (Shalele)

Matsala ta da manema aure na - Shalele Umar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!