• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 22, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Magoya bayan Atiku sun yi wa taron gwamnonin PDP ‘yan G5 ƙafar angulu a Legas

by DAGA WAKILIN MU
November 22, 2022
in Nijeriya
0
Gwamnonin G5 a wurin taron su a Legas

Gwamnonin G5 a wurin taron su a Legas

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TARON hasalallun gwamnonin PDP biyar masu neman a cire Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya samu tangarɗa.

Taron, wanda aka gudanar a ofishin tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Olabode George, a Ikeja, ya samu halartar dukkan gwamnoni biyar masu adawa da shugabancin Ayu. 

Rashin amincewar su da Ayu ne ya kai su ga ƙaurace wa rangadin neman zaɓen shugaban ƙasa da Atiku Abubakar ya fara.

Gwamnonin biyar su ne Nyesom Wike na Jihar Ribas, Samuel Ortom na Binuwai, Seyi Makinde na Oyo, Ifeanyi Ugwuanyi na Inugu da Okezie Ikpeazu na Abiya.

A ranar Litinin ce su ka yi sanarwar kafa ƙungiyar G5, kuma su ka kira ta da ‘Integrity Group’, wadda su ka kafa da niyyar abin da su ka kira “saita PDP kan turbar yin adalci.”

Sai dai kuma wasu gungun magoya bayan Atiku da PDP sun hana taron gwamnonin biyar yin armashi.

A wurin taron, magoya bayan ɗan takarar sun riƙa rera take da kirarin “Atiku! Atiku! Atiku!” da ƙarfi a daidai lokacin da George ya fara bayanin cewa ba za su yi zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnonin PDP ba, amma za su yi zaɓen ‘yan Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai.

Membobin PDP na Jihar Legas sun halarci taron saboda sun gano akwai maƙarƙashiyar da ake zargin Bode George ya shirya domin ya karya lagon Atiku.

Ɗaya daga cikin membobin PDP a Legas mai suna Kunle Folorunsho ya saki wani bidiyo da ke tabbatar da cewa ya halarci taron, kuma akwai hayaniyar da ta kaure wurin taron duk a cikin gajeren bidiyon.

Ya ce yayin da George ya ke cikin bayanin cewa su ba za su zaɓi Atiku ba, nan da nan sai shi kuma ya miƙe tsaye ya ƙalubalance shi da cewa ai PDP ta na da ɗan takarar ta, Atiku Abubakar, kuma shi za su zaɓa.

Folorunsho ya ce tun bai gama rufe baki ba sai magoya bayan George su ka dira kan sa, su ka kekketa masa riga. 

Ya ce: “Da ƙyar wasu magoya bayan Atiku su ka cece ni daga hannun magoya bayan Bode George.” 

Yayin da gwamnonin ke shirin fita daga ɗakin taron, Folorunsho ya ce dandazon jama’ar da ke waje ba su samu shiga ba sun riƙa rera “sai Atiku, sai Atiku, sai Atiku!”

Hakan da aka yi, a cewar Folorunsho, ya nuna hasalallun gwamnonin biyar ba za su iya raba kan ‘yan PDP a jihar ba.

Gwamnonin G5, tare da sauran hasalallun magoya bayan su, sun shafe sama da awa uku su na tattauna matakin da za su ɗauka a gaba.

Tsohon gwamnan Filato, Jonah Jang, shi ne ya yi magana a madadin sauran gwamnonin, kuma ya ce har yanzu su na kan matsayar da su ka cimma a taron su na Fatakwal, inda su ka ce “ƙofar yin zaman sulhu da mu a buɗe ta ke.”

Sauran waɗanda su ka halarci taron na Legas kuma masu goyon bayan G5 sun haɗa da Sanata Olaka Nwogu, Sanata Ohuabuwa, Sanata Nazifi Suleiman, Bello Adoke, Segun Mimiko, Ayo Fayose, Donald Duke da sauran su.

Loading

Tags: Atiku AbubakarBode GeorgeG5LegasNyesome WikePDPTaroZaɓen 2023
Previous Post

KILAF 2022: Yau za a fara Bikin Baje-kolin Finafinan Harsunan Afirka na Kano

Next Post

Alƙawarin Atiku ga Gombawa: Zan farfaɗo da dam ɗin Daɗin Kowa, samar da lantarki, noman rani da titina

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Atiku na amsar gaisuwa daga magoya bayan sa a Gombe

Alƙawarin Atiku ga Gombawa: Zan farfaɗo da dam ɗin Daɗin Kowa, samar da lantarki, noman rani da titina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!