ALLAH ya yi wa mahaifin tsohon shugaban ƙungiyar dillalan kaset ta Jihar Kano, Alhaji Ahmad Muhammad Amge, rasuwa.
Dattijon, Malam Muhammadu Tunau, ya rasu ne a ranar Juma’a da ta gabata, 11 ga Yuni, 2021, a garin Ɗanchadi da ke Ƙaramar Hukumar Boɗinga a Jihar Sokoto, sakamakon ciwon ciki da ya kama shi a ranar.
Ya rasu ya bar ‘ya’ya da jikoki masu yawa.
Alhaji Amge da kan sa ne ya bada sanarwar rasuwar a yau a Facebook.
A saƙon da ya wallafa, babban ɗan kasuwar kuma furodusa ya ce, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Allah ya yi wa mahaifi na rasuwa ranar 11/6/2021 bayan ya kammala sallar Juma’a a sanadiyyar ciwon ciki. Allah ya jiƙan baban mu da rahama, amin!”

Ɗimbin masu harkar fim da sauran jama’a sun yi masa gaisuwa tare da addu’ar Allah ya jiƙan mahaifin nasa.
Mu ma a mujallar mu na addu’ar Allah ya rahamshe shi, ya kyautata zuri’ar da ya bari, amin.
Shi dai Amge, ya jagoranci ƙungiyar ‘yan kasuwa masu sayar da finafinai fa waƙoƙin Hausa ta Jihar a lokacin da harkar fim ke ci sosai.
A lokacin, ana sayar da finafinai a kaset ɗin VHS ne, kafin daga baya a koma sayarwa a faifan sidi, daga nan kuma aka koma dibidi.
Shigowar soshiyal midiya ce ta karya dukkan ‘yan kasuwar, wanda hakan ya sa kasuwar finafinai ta ɓace.