INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya yi wa mahaifin fitacciyar jaruma Ladi Mohammed (‘Mutu-ka-raba’) rasuwa.
Malam Isa, wanda aka fi sani da Isa Masta, ya rasu ne daren jiya Laraba, 25 ga Disamba, 2019 a asibitin ‘City Clinic’ da ke Titin Zariya a cikin garin Kano.
Marigayin, mai shekara kusan 100 a duniya, ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Ya rasu ya bar ‘ya’ya 16. Sun haɗa da ita Ladi Mutu-ka-raba da fitaccen ɗan wasan ƙoroso ɗin nan a Hukumar Tarihi da Al’adu ta Jihar Kano, wato Saminu Cuwa-cuwa.
An dai yi jana’izar marigayin a gidan sa da ke garin Dakatsalle a Ƙaramar Hukumar Bebeji a cikin Jihar Kano.
Allah ya rahamshe shi, amin.