ALLAH ya ɗauki ran mahaifiyar furodusa a Kannywood kuma mataimakin shugaban ƙungiyar furodusoshin Kannywood ta Nijeriya (KPAN), Dakta Abdallah Tahir Ahmad Kenana.
Hajiya A’isha Muhammad Hamza ta rasu ne a jiya Juma’a bayan ta yi buɗe-baki a ƙasar Saudiyya.
Mujallar Fim ta samu labarin cewa bayan buɗe-bakin ne sai Hajiya ta ji ƙirjin ta yana zafi, sai aka kira maƙwabciyar ta, kafin ta zo inda take rai ya yi halin sa. Ba rashin lafiya ta yi ba.
Dattijuwar ta rasu ta bar ‘ya’ya uku, maza biyu da mace ɗaya. Dr. Abdallah, wanda shi ne tsohon Darakta-Janar na Hukumar Ƙayata Birane ta Jihar Kano, shi ne na ukun.
An yi jana’izar Hajiya A’isha a Saudiyya.
Allah ya gafarta mata, ya albarkaci dukkan abin da ta bari.
![]()






