ALLAH ya yi wa Hajiya Hauwa Muhammadu Dodon Aku, mahaifiyar tsohon Editan mujallar Fim, Malam Sani Mohammed Maikatanga, rasuwa.
Marigayiyar mai shekaru 70 ta rasu a daren Litinin, 16 ga Yuni, 2025 a gidan ta da ke Unguwar Madaki, bayan gidan Sarkin Gumel a cikin garin Gumel na Jihar Jigawa.
An yi jana’izar ta a jiya Talata, da misalin ƙarfe 7 na safe.
Ta rasu ta bar ‘ya’ya uku: Haruna, Jamila, da Sani Maikatanga.
Sani Maikatanga dai ƙwararren mai ɗaukar hoto ne wanda ya ci gasannin ɗaukar hoto a gida Nijeriya da ƙasashen waje.
A gobe ne za a yi addu’ar uku a Unguwar Madaki da ke Gumel.
Allah ya jiƙan Hajiya Hauwa, ya ba iyalai haƙurin jure wannan babban rashi, amin.