• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 23, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mai neman zama gwamnan Neja a APC, Mohammed Malagi, ya yi alƙawarin kula da haƙƙin mata da matasa

by DAGA WAKILIN MU
February 23, 2022
in Nijeriya
0
Alh. Mohammed Idris Malagi (a dama) ya na zantawa da Haliru Zakari Jikantoro a sakatariyar jam'iyyar a Minna jiya

Alh. Mohammed Idris Malagi (a dama) ya na zantawa da Haliru Zakari Jikantoro a sakatariyar jam'iyyar a Minna jiya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, wanda ke neman tsayawa takarar gwamnan Jihar Neja a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya yi alƙawarin cewa idan har ya ci zaɓe zai kula da haƙƙin mata da matasa a gwamnatin sa.

A yayin da ya ke jawabi ga shugabannin jam’iyyar lokacin da ya kai masu ziyara a ranar Talata a Minna, Malagi ya ce: “Za mu ci gaba da bai wa mata da matasa kyakkyawar kulawa kamar yadda ya kamata. 

“Babu yadda za a yi mu cimma nasarar gudanar da mulkin dimokiraɗiyya ko wani tsari na siyasa ba tare da mun sako mata da matasa a cikin tafiyar ba. Mu na goyon bayan mata da matasa. Mun yarda da ku ainun.”

Bayan ya kira kan shi da “wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar APC tun daga farkon ta”, sai kuma ya ce, “Na tsaya nan a gaban ku ne a yau saboda duk mun zaɓi mu kasance masu biyayya, masu tsare gaskiya, kuma nagartattun ‘ya’yan gagarumar jam’iyyar mu ta APC. Ba kawai kirarin jam’iyya ko tutar ta ba ne su ka haɗe mu a waje guda ba, a yau mun zama babban gida na ƙasa baki ɗaya. A Jihar Neja, APC ce jam’iyyar da ta fi kowace jam’iyya da mu ka gani tun daga 1999.” 

Malagi tare da shugabannin APC na Jihar Neja lokacin tattaunawar su

Malagi ya kuma yaba wa gwamnan jihar, wato Alhaji Abubakar Sani Bello, saboda yadda ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa APC ta zama gagarumar jam’iyya a Jihar Neja.

Haka kuma ya taya murna ga shugaban APC na jihar, Alhaji Haliru Zakari Jikantoro, da kuma shugabannin ta na matakan yanki da ƙananan hukumomi da wad-wad saboda nasarar zaɓe da kuma rantsarwa da su ka samu kwanan nan.

Ya bayyana zaɓen Jikantoro a matsayin ciyaman ɗin jam’iyyar na jiha da cewa “sabon alfijir ne da ya keto na ingantantacciyar dimokiraɗiyya a Jihar Neja.”

Ya ƙara da cewa, “Ina addu’ar Allah ya sa wannan nasara ta zama abin da zai kawo ƙarin nasarori a rayuwa da kuma harkar siyasa.”

Alhaji Mohammed Malagi ya faɗa wa shugabannin jam’iyyar cewa: “Yanzu mulkin dimokiraɗiyyar jam’iyya ya na hannun ku. Mu na da tabbacin ku na da basirar yi wa Jihar Neja aikin da za a yi alfahari da ku.”

Ya tunatar da shugabannin cewa shi ma ya jima ya na tallafa wa APC a Jihar Neja saboda ya yi amanna da cewa ita ce “jam’iyyar jama’a daga kowane ɓangare na rayuwa.”

Ya ce, “Shi ya sanya na ke tabbatar da ganin ana ɗorawa a kan nasarorin da ta ke samu, tare da biyan kuɗin hayar ofisoshin ta na jiha da na yankuna. Ba zan gaji ba a wannan hoɓɓasa na nuna biyayya. Kuma zan ci gaba da tallafa wa ayyukan jam’iyya a duk lokacin da aka buƙace ni.

“Ya shugaba, mun zo nan wurin ne a yau da niyyar mu taya ku murna sannan kuma mu  ba ku cikakkiyar girmamawa, mu karrama dukkan shugabannin jam’iyya yadda ya kamata saboda mu ‘ya’yan APC ne, mu iyalai ne abin sha’awa.

“Su kuma masoya tare da masu taya Malagi murna, waɗanda su ka zo nan a yau domin mu yi taron murnar nasarar APC tare, ina maku marhabin kuma ina gode maku saboda tsantsar amincin ku da soyayya da kuma goyon bayan da ku bayarwa ba tare da gajiyawa ba.”

A lokacin wannan ziyarar dai, mai neman zama ɗan  takarar ya bayyana “wata ‘yar gudunmawa” don samun cigaba, haɗin kai da ɗorewar jam’iyyar, inda ya ba ta kyautar naira miliyan 43 tare da motocin safa guda 31.

Malagi ya ce ya bada kyautar ne saboda a ƙara ƙarfafa jam’iyyar a jihar.

Yadda aka raba gudunmawar shi ne:  motocin safa ƙirar Sharon guda 3 da kuma naira miliyan 15 ga sakatariyar jam’iyyar ta jiha, sai mota 1 ƙirar Sharon haɗi da kuɗi naira miliyan 1 ga kowane ofishin yanki na jam’iyya.

Haka kuma ya ba ofishin jam’iyya a kowace daga cikin Ƙarananan Hukumomi 25 na jihar kyautar mota Sharon haɗi da naira miliyan 1. Kuɗin sun kama naira miliyan 25 da kuma motocin Sharon guda 25 kenan.

Wani sashe na mahalarta taron

Malagi ya yi amfani da wannan dama ya miƙa ta’aziyyar sa ga al’ummar jihar bisa rasuwar tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Isah Ibrahim Ladan, wanda ya ce “ƙwararren ma’aikaci ne.”

Haka kuma ya jajanta wa shugabannin jam’iyyar tare da addu’ar Allah ya ba su haƙurin jure wannan babban rashi.

Malagi ya kuma bayyana alhini kan kisan killar da ‘yan ta’adda su ka yi wa   wasu jami’an Hukumar Rundunar Tsaron Nijeriya (NCDC) a Shiroro kwanan nan, ya ce, “Allah ya jiƙan su da rahama.”

Malagi (a hagu) da Jikantoro su na gabatar da jawabin su a taron
Alh. Mohammed Idris Malagi ya na amsa gaisuwar dandazon masoyan sa a sakatariyar APC da ke Minna jiya. Hotuna daga: Jibrin Baba Ndace

Loading

Tags: Abubakar Sani BelloAlhaji Mohammed Idris MalagiAll Progressives CongressAPCBlueprintgudunmawaHaliru Zakari JikantoroIsah Ibrahim Ladanjam'iyyaJhar NejaMalagiManhajamatamatasaMinnaNCDCNigeria Civil Defence CorpstallafiZaɓen 2023
Previous Post

Za mu riƙa ba furodusoshi jiragen ƙasa kyauta don su shirya finafinai, inji Amaechi

Next Post

Abin ya zo! Za a ɗaura auren jarumar Kannywood Hassana Muhammad da furodusa Bashir Maishadda

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Hassana Muhammad da Abubakar Bashir Maishadda

Abin ya zo! Za a ɗaura auren jarumar Kannywood Hassana Muhammad da furodusa Bashir Maishadda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!