‘Maimuna Gandama’ fim ne mai yanka-yanka (series) da kamfanin Raliya Entertainment da haɗin gwiwar Hijra Multimedia su ka shirya. Shahararren marubuci Zubairu Musa Balannaji ne ya rubuta labarin ya tsara shi. Hajiya Sadiya ce ta ɗauki nauyin shiryawa daga Amina Baby yayin da darakta Baffa M. Shareef ya bada umarni.
Taurarin shirin sun haɗa da Alasan Kwalle, Ahmed Tage, Hamza Indabawa, Sani Garba SK, Muhammad Usman, Hajjo Mama, Hajiya Sadiya (Maimuna Gandama), Haj. Zahra’u, Bilkisu Baba, A’isha Ashmat, Hadiza Gombe da sauran su.
Tun a farkon shirin an nuna Maimuna Gandama a matsayin wata yarinya a karkarar su marar jin magana da rashin natsuwa. Ba ta ganin kan kowa da gashi. In dai ba kuɗi mutum zai ba ta ba, ba ya ganin murmushi ko fara’ar ta.
Duk da wannan hali nata, ta na da farin jinin samari. Duk da yake akwai wanda ta ke so, Maimuna ta yi alƙawarin samo wa saurayin ta kuɗi don ya ji daɗin rayuwa, domin a cewar sa ba zai iya rayuwar ƙauye ba.
Iyayen ta su na ƙoƙarin ta gyaru, amma abu ya gagara.A ƙarshen yanka na ɗaya (episode 1) ya ƙare ne a inda Maimuna ta karɓi kuɗi daga wurin Alasan Kwalle.
Fim ɗin an shirya shi ne bisa doron rayuwar ƙauye, rayuwar ma wai irin ta Bahaushe, amma sai ga shi babu ta inda ake tallata kyawawan al’adun Bahaushe, musamman na kauye, bilhasli ma akasi aka nuna, wanda sanin kowa ne ya na daga manufofin yin fim – tallata al’adun masu fim ɗin.
1. An nuna Maimuna ta na cin abu a gaban Alasan Kwalle yayin da su ke taɗi. Yin haka ba daidai ba ne.
2. ‘Yanmatan da su ka je gidan su Maimuna kai ƙarar Maimuna ta fasa musu tuluna a rafi sun yi wa babar Maimuna rashin kunya, wanda zai yi wahala yara masu tarbiyya irin ta ƙauye su gaya wa babba irin waɗannan maganganun, har da tsayawa tsage-tsage a gaban ta kamar wasu sa’annin ta.
3. Ita kan ta jarumar labarin, yanayin shekarun ta ta yi tsufan da za ta fito a wannan matsayin. Ina laifin a samu yarinya matashiya?
4. Sauti ya samu matsala a labarin ta yadda iska ta ke yawan shiga maɗaukar sautin. Hoto ya kan yi rawa a wasu wuraren.
5. Shi kan sa labarin babu cikakkiyar gabatarwa ga taurari ta yadda mai kallo zai fahimci matsayin tauraro daga zarar ya bayyana.
Da fatan za a gyara a yanka na gaba.