JARUMI kuma furodusa a Kannywood, Abdulwahab Alhassan (Awarwasa), mutum ne wanda ya kasance mai bin duk umarni ko hanin da yayyen sa su ka yi masa kan wani lamari da ya taso, walau wanda ya shafi gida ne ko waje.
Yayan sa da ya ke bi, Abdulrazak Alhassan, shi ne ya faɗa wa mujallar Fim hakan jim kaɗan bayan an gama jana’izar marigayin a Kano a yau Talata, 24 ga Janairu, 2023.
Kamar yadda mujallar Fim ta riga ta ruwaito, Allah ya karɓi ran Awarwasa ne a jiya Litinin a wani asibitin kuɗi da ke Jos, Jihar Filato, bayan ya shafe tsawon lokaci ya na fama da jinya.
An iso da gawar sa Kano da misalin ƙarfe 2 na daren jiya, aka yi masa sallah a ƙofar gidan su da da ke unguwar Bakin Kurmi, Layin ‘Yan Kabewa, a cikin birnin Kano, da misalin ƙarfe 9:13 na safiyar yau.
Daga nan kuma aka kai shi gidan sa na gaskiya da ke maƙabartar da ke daura da babbar mayankar Kano, wato Abbatuwa, da ke Ƙofar Mazugal.
Wani abin juyayi kuma shi ne an binne marigayin a tsakanin ƙaburburan mahaifin sa da mahaifiyar sa da kuma wani ƙanen mahaifin sa waɗanda sun daɗe da rasuwa.
Biyu daga cikin yayyen marigayin da su ka kasance a wurin, sun bayyana wa mujallar Fim cewa marigayin ya na da kyawawan halaye da su ka haɗa da biyayyar da ya kasance ya na yi masu.

Abdulrazak Alhassan, wanda Awarwasa ke bi a cikin yayyen, ya faɗa wa wakilin mu cewa duka iyayen su sun daɗe da rasuwa. Mahaifiyar su ce ta fara rasuwa, sai mahaifin su.
Ya ce su huɗu ne a wurin mahaifiyar su – mata biyu, maza biyu, sai sauran ‘yan’uwan su.
Awarwasa dai ya shafe kusan shekara 20 a Kannywood, ya kuma rasu ya na da shekara 43 a duniya. Ya bar mata ɗaya da ‘ya’ya uku.
Duk da daɗewar da ya yi a masana’antar shirya finafinai, tauraruwar sa ba ta daɗe da fara ɗagawa ba, domin kuwa an fara sanin shi sosai ne bayan shigowar yayin finafinai masu dogon zango, musamman waɗanda su ka ƙunshi harkar daba a cikin su, irin su ‘A Duniya’, ‘Sanda’, ‘Lokaci’, ‘Madugu’, ‘Ɗan Jarida’ da wasu daga cikin finafinai da aka saba yi a baya.
Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka halarci jana’izar sun haɗa da Tijjani Asase, Abubakar Bashir Maishadda, Abdul Amart, Nasiru Ali Ƙoƙi, Naziru Ɗanhajiya, Tahir Fagge, Daddy Hikima (Abale), Abdullahi Nalako, Ɗanjuma Salisu, Ali Gumzak, da Ghali Ibrahim ‘Yandoya.
Allah ya jiƙan shi da rahama, amin.


Comments 1