• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Marigayi Awarwasa mutum ne mai biyayya ga na gaba da shi, inji yayan sa

by DAGA AHMAD A. UMAR
January 24, 2023
in Labarai
1
Abdulwahab Awarwasa (a hagu). Ana addu'a a gaban kabarin sa

Abdulwahab Awarwasa (a hagu). Ana addu'a a gaban kabarin sa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMI kuma furodusa a Kannywood, Abdulwahab Alhassan (Awarwasa), mutum ne wanda ya kasance mai bin duk umarni ko hanin da yayyen sa su ka yi masa kan wani lamari da ya taso, walau wanda ya shafi gida ne ko waje.

Yayan sa da ya ke bi, Abdulrazak Alhassan, shi ne ya faɗa wa mujallar Fim hakan jim kaɗan bayan an gama jana’izar marigayin a Kano a yau Talata, 24 ga Janairu, 2023. 

Kamar yadda mujallar Fim ta riga ta ruwaito, Allah ya karɓi ran Awarwasa ne a jiya Litinin a wani asibitin kuɗi da ke Jos, Jihar Filato, bayan ya shafe tsawon lokaci ya na fama da jinya.

An iso da gawar sa Kano da misalin ƙarfe 2 na daren jiya, aka yi masa sallah a ƙofar gidan su da da ke unguwar Bakin Kurmi, Layin ‘Yan Kabewa, a cikin birnin Kano, da misalin  ƙarfe 9:13 na safiyar yau. 

Daga nan kuma aka kai shi gidan sa na gaskiya da ke maƙabartar da ke daura da babbar mayankar Kano, wato Abbatuwa, da ke Ƙofar Mazugal.

Wani abin juyayi kuma shi ne an binne marigayin a tsakanin ƙaburburan mahaifin sa da mahaifiyar sa da kuma wani ƙanen mahaifin sa waɗanda sun daɗe da rasuwa.

Biyu daga cikin yayyen marigayin da su ka kasance a wurin, sun bayyana wa mujallar Fim cewa marigayin ya na da kyawawan halaye da su ka haɗa da biyayyar da ya kasance ya na yi masu.

Kabarin Awarwasa kusa da na iyayen sa

Abdulrazak Alhassan, wanda Awarwasa ke bi a cikin yayyen, ya faɗa wa wakilin mu cewa duka iyayen su sun daɗe da rasuwa. Mahaifiyar su ce ta fara rasuwa, sai mahaifin su.

Ya ce su huɗu ne a wurin mahaifiyar su – mata biyu, maza biyu, sai sauran ‘yan’uwan su.

Awarwasa dai ya shafe kusan shekara 20 a Kannywood, ya kuma rasu ya na da shekara 43 a duniya. Ya bar mata ɗaya da ‘ya’ya uku.

Duk da daɗewar da ya yi a masana’antar shirya finafinai, tauraruwar sa ba ta daɗe da fara ɗagawa ba, domin kuwa an fara sanin shi sosai ne bayan shigowar yayin finafinai masu dogon zango, musamman waɗanda su ka ƙunshi harkar daba a cikin su, irin su ‘A Duniya’, ‘Sanda’, ‘Lokaci’, ‘Madugu’, ‘Ɗan Jarida’ da wasu daga cikin finafinai da aka saba yi a baya.

Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka halarci jana’izar sun haɗa da Tijjani Asase, Abubakar Bashir Maishadda, Abdul Amart, Nasiru Ali Ƙoƙi, Naziru Ɗanhajiya, Tahir Fagge, Daddy Hikima (Abale), Abdullahi Nalako, Ɗanjuma Salisu, Ali Gumzak, da Ghali Ibrahim ‘Yandoya.

Allah ya jiƙan shi da rahama, amin.

Tarin jama’a maƙabartar da aka kai Awarwasa
Su Maishadda a wurin zaman makoki

Loading

Previous Post

Zaɓen 2023: INEC ta hana ma’aikatan ta shiga cuwa-cuwa wajen raba katin rajistar zaɓe

Next Post

Jarumin Kannywood Aminu Mirror ya samu ƙaruwar ‘ya mace

Related Posts

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
Next Post
Malam Aminu Shehu Mirror da jaririya da aka haifa masa

Jarumin Kannywood Aminu Mirror ya samu ƙaruwar 'ya mace

Comments 1

  1. Pingback: An Bayyana Wasu Kyawawan Halayen Marigayi Jarumi Awarwasa – Dimokuradiyya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!