WANI masanin harshen Hausa ɗan ƙasar Nijar Dakta Korao Hamadou ya gabatar da waɗansu haruffa a Kano waɗanda ya ce su ne baƙaƙen rubutun Hausa na asali tun kafin zuwan rubutun ajami ko abacada na Turawa.
Ya gabatar da su ɗin ne a maƙalar da ya gabatar a wurin wani taron wuni guda da aka gudanar da a ɗakin taro na CBN Centre da ke cikin sabuwar Jami’ar Bayero da ke Kano.
A taron, wanda ya samu halartar manyan malamai da masana a kan harshen Hausa daga sassa daban-daban na duniya, Dakta Hamadou ne babban baƙo mai jawabi.
Ya ce sababbin haruffan “an samo alamomin su ne daga masu bayar da magungunan gargajiya ta hanyar taskace sassaƙe da saiwoyi da ganyaye da kauci da kuma ɓawo.”
Malamin ya gabatar da waɗannan alamomi a gaban manyan malaman harshen Hausa, inda ya kafa hujja da cewa irin waɗannan alamomi su ne na farko a wajen samar da rubutu a duniya.
Masanin ya kawo sunayen manyan litattafan tarihi da na Musulunci da suke nuna cewa lallai Hausawa ne suka fara samar da wani abin rubutawa da irin waɗannan alamomi.
Haka kuma ya kawo misalai da dama a kan yadda za a yi amfani da haruffan da yadda za su bunƙasa idan ana amfani da su.

Manyan malaman Hausa da na Tarihi sun tafka muhawara a kan waɗannan alamomi.
Ɗaya daga cikin su, Farfesa Hafizu Miko Yakasai, ya ƙalubalanci Dakta Ahmadu a kan haruffan ta yadda ba su samu sahalewar manyan malaman Hausa ta hanyar gabatar da su ba.
Ya ce idan ta hanyar masu bada magani ko itatuwa da kauci da ganye aka same su, to ai akwai tsofaffin hanyoyi na sana’o’i irin su ƙira, fawa, da dukanci, to su kuma ina irin nasu yake?
An shafe tsawon lokaci ana yi masa tambayoyi, yayin da shi kuma a dunƙule ya bada amsa da cewar wannan wani ɓangare ne na ilimi mai zurfi da haruffan suke ɗauke da shi, kuma ilimi sirri ne da shi don haka bai kamata ya bayyana shi ba tun kafin lokacin ƙaddamar da shi ba.
Ya ce a jira lokacin da za a ƙaddamar da shi, saboda akwai sauran nazari da bincike da yake yi kafin ya saki ilimin ga al’ummar duniya.
Ana sa ran nan gaba za a yi wani taron masana ilimin kimiyyar harshe da masana tarihi da al’adu domin samar da matsaya a kan waɗannan alamomi.

Hotunan Rubutun Hausa na Asali Da Dakta Korao Hamadou Ya Kawo a Taron
