A DAREN shekaranjiya Asabar, Allah ya ɗauki ran mataimakin shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) reshen Jihar Zamfara, Alhaji Sani Shehu, wanda aka fi sani da Ɗan Fim.
Malam Sani ya rasu da misalin ƙarfe 11:30 na dare, a wani asibiti a Ilorin, Jihar Kwara, bayan doguwar jinya da ya yi.
An yi jana’izar sa a jiya Lahadi da misalin ƙarfe 8:00 na safe, a Jihar Kwara.
Marigayin, mai kimanin shekara 45, ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya biyar.
Kafin rasuwar sa, Alhaji Sani shi ne Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Wasa (Actors Guild) ta Jihar Zamfara.
Allah ya jiƙan sa da rahama.