TUN kusan makon ƙarshe na shekarar 2020 wasu daga cikin ‘yanmatan Kannywood su ka fara lulawa zuwa Dubai domin hutun ƙarshen shekara kamar yadda su ka saba yi a kowace shekara.
Jaruman dai sun haɗa da Hadiza Gabon, Fati Washa, Rahama Sadau tare da ƙannen ta Zainab, A’isha da Fatima, sai kuma Nafisat Abdullahi, Hafsat Idris (Ɓarauniya) tare da ‘yar ta Ramlat, Maryam Waziri, Maryam A.B. Yola, Sabira Mukhtar da sauran su.
Da alama sun maida abin kamar al’ada, da zarar sun sauƙa a ƙasar da duk su ka je, za su yi ta ɗaukar hotuna su na rige-rigen sakawa a shafukan su na soshiyal midiya don duniya ta gani.
An gan su sanye da ƙananan kaya a wuraren shaƙatawa da buɗe ido daban-daban a birnin Dubai, wanda ya haɗa da wasa a kan wasu baburan ruwa a cikin wani makeken tafki, da yawon buɗe ido a kan tituna da katafaren shaguna, da kuma cin abinci a manyan wuraren cin abinci irin su Bosphorus Restaurant.

Gabon, Rahama da Washa sun haɗa kan su, inda duk ka ga zara ka ga wata, kamar dai yadda su ka yi a shekarar 2019 a ƙasar Ingila. Wannan ya nuna cewa su na da kyakkyawar alaƙa a tsakanin su.
Sauran jaruman kuma kowacce ta kan ta ta ke yi, domin babu inda aka gan su tare da abokan sana’ar su.
Wani abin burgewa shi ne a ranar Juma’a, 1 ga Janairu, 2021 aka karrama Rahama Sadau a wani fitaccen gidan abinci mai suna CZN Burak da su ka yi wani burodi mai ɗauke da sunan ta.
Gidan abincin sun saba yi wa manyan gwarzaye irin wannan karramawar, domin kuwa hatta fitaccen ɗan ƙwallon ƙafar nan ɗan ƙasar Potugal, mai taka leda a kulob ɗin Juventus, wato Cristiano Ronaldo, ya taɓa samun irin wannan karramawar. A nan ana iya cewa Rahama ce ta farko a Nijeriya, kuma ta huɗu a duniya da aka yi wa hakan.
Jarumar ta samu wannan karramawa ne ba zato ba tsammani, domin kuwa bayan sun gama cin abinci tare da ƙawayen ta ne manajan gidan abincin Burak Ozdemir ɗan asalin ƙasar Turkiyya ya shammaci jarumar ya gabatar mata da burodin karramawar mai ɗauke da sunan ta a jiki.
Jarumar ta nuna farin cikin ta matuƙa, kuma ta yi godiya da karramawar da aka yi mata.

Bayan Rahama kuma, ita ma Nafisat Abdullahi an yi mata irin wannan karramawar ta buga sunan ta a kan burodi a dai wannan gidan cin abincin.
Idan kun tuna, a shekarar bara sai da mujallar Fim ta yi rahoto kan irin wannan yawon buɗe da matan Kannywood ke yi, a cikin wani rahoton musamman.
A rahoton, Fim ta lura da wasu abubuwa biyu: mata ‘yan fim kaɗai ne ke zuwa yawon buɗe ido a ƙasar waje, babu namiji ko ɗaya, sannan kuma ta yi tambaya kan inda su ke samun miliyoyin nairar da su ke kashewa wajen wannan balaguron na raƙashewa.

Mujallar ta bar wa masu karatun ta sani.