• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mauludi: Duk da ruwan sama ya hana, na ga taron masoya Annabi – Sayyada Raihan Imam Kamshi

by MUKHTAR YAKUBU
September 23, 2025
in Addini
0
Mauludi: Duk da ruwan sama ya hana, na ga taron masoya Annabi – Sayyada Raihan Imam Kamshi

Sayyada Raihan Imam Kamshi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A sakamakon wani ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi a birnin Kano da kewaye a ranar Asabar 20 da ta gabata, an samu ya tsaiko a taron bikin Maulidin Manzon Allah (s.a.w.) wanda Sayyada Raihan Imam Ƙamshi ta shirya. Jarumar ta Kannywood ta saba gabatar da taron Maulidi a duk shekara.

An dai tsara za a fara taron da misalin ƙarfe 7 na yamma zuwa abin da ya sauwaƙa. An kammala komai, kamar tsara wajen da rumfuna da kujeru na alfarma, ga dardumomi masu ɗaukar hankali saboda manyan baƙi da sauran abubuwa masu ƙayatarwa.

Ruwan sama ya tsuge tun daga ƙarfe 6 har zuwa tsakiyar dare. Wannan ya sa komai na taron ya tsaya, ana jiran lokacin da ruwan zai tsaya, amma sai ya ci gaba babu ƙaƙƙautawa; da man ga shi iska ta wargaza wajen. Don haka taron ya kasa yiwuwa.

Sai dai duk da haka ɗimbin jama’a masoya Manzon Allah sun yi ta zuwa a cikin ruwan domin nuna shauƙin su. Don haka jama’a ta taru a cikin gidan su Raihan Imam Ƙamshi har zuwa ƙofar gida, mutane ne ba masaka tsinke, ga
sha’irai da ‘yan fim da sauran jama’ar gari. Duk wanda ka gani a jiƙe yake, sai dai wanda ya saka rigar ruwa.

Dangane da yadda taron ya kasance, mujallar Fim ta nemi jin ta-bakin Sayyada Raihan, kuma ta amince ta tattauna da mu kamar haka:

FIM: Ga shi dai yau kika tsara za ki gudanar da taron Maulidi, amma ruwan sama ya hana. Ko ya kike ji yanzu?

RAIHAN IMAM ƘAMSHI: To alhamdu lillah! Ka ga dai yadda taron ya zama, mun gama shirya komai, an haɗa waje an saka duk abin da ya kamata a saka, muna daf da mu fara sai aka samu saukar ruwan sama mai ƙarfi da iska. Hakan ya sa wajen ya lalace, don abubuwan da aka kafa iska ta ture su, wasu abubuwan da aka liƙa isaka ta yage su. Tun muna tunanin za a ɗauke ruwa mu yi da abin da ya samu sai ruwa bai ɗauke ba.

Ga kayan da za mu raba a wajen, ga abinci da za a raba, duk an kammala, domin akwai kyautuka da za a raba wa masoya Annabi da za su halarci wajen, sai dai yanayin saukar ruwan saman bai sa abin ya tafi a yadda muka tsara ba. Wannan al’amari ne na Allah, Shi yake tsara yadda Ya so a lokacin da Ya so.

FIM: Hakan ne ya sa komai ya tsaya kenan?

RAIHAN: To ba za a ce komai ya tsaya ba. Duk da haka babu abin da zan ce da Allah sai godiya, domin kuwa duk da ruwan da aka yi jama’a masoya Manzon Allah (s.a.w.) sun halarci wajen fiye da yadda nake tunani.

Ana ruwa mutane suna ci gaba da zuwa. Unguwar mu ta cika da motocin mutane masu zuwa wajen Maulidin; wasu sun saka rigar ruwa, wasu kuma babu rigar ma haka suka taho a jiƙe, duk wanda ka gani a wajen a jiƙe yake. Tun ana shiga cikin gida, sai gidan ya cika, mutane suka rinƙa tsayawa a waje, nan ma dai layin namu ya cika. Kai, abin dai sai godiya ga Allah, domin lamarin Annabi daban ne!

Ni kai na na yi mamakin kai na. Duk da ba na son shiga ruwa, haka na fito ina taryar baƙi cikin ruwan, na jiƙe sharkaf, saboda mutane zuwa suke har zuwa ƙarfe 1 na dare, wanda ko da taron Mauludin ma za a yi to iya lokacin da za a tashi kenan.

FIM: Wane darasi kika samu a wannan taron Mauludin?

RAIHAN: To gaskiya na samu darasi sosai, domin ka ga duk shekara na saba shirya taron Mauludin a duk ranar 27 ga Rabi’ul Awwal, amma ba a samu lokacin da ya haɗe da ruwan sama ba sai na wannan shekara. To ka ga wannan darasi ne da yake nuni da ita rayuwa; ba ko da yaushe abin da ka shirya ko kake so kuma yake samuwa ba. Idan son samu na ne, na yi taron Mauludin kamar yadda na tsara, sai kuma Allah ya sa ruwa ya sauka. Kuma na yi shiri sosai a wannan shekarar fiye da yadda na saba yi a baya. Su kan su jama’ar a yadda na gani da ba a samu saukar ruwan ba, to yawam su sai ya fi na baya, ka ga wannan ma darasi ne. Muna fatan Allah ya kai mu na shekara mai zuwa cikin ƙoshin lafiya.

Kuma ina godiya ga manyan malamai da suka halarci wajen taron duk da ruwan da aka yi. Haka nan sha’irai su ma na gode sosai. Allah ya ƙara kusanci da Annabi.
Su ma abokan sana’a ta ‘yan fim da daman su sun zo, don haka ina godiya a gare su. Allah ya bar zumunci. Allah ya ƙara mana son Manzon Allah (s.a.w.).

FIM: To, madalla. Mun gode.

RAIHAN: Ni ma na gode sosai.

Loading

Previous Post

An fitar da ƙa’idojin gasar Ranar Marubuta ta Duniya 2026

Next Post

Ƙungiyar ‘yan fim ta Matan Mu A Yau ta yi taron farfaɗowa

Related Posts

Abin da ya sa Hukumar Tace Finafinai take gudanar da taron Mauludi – El-Mustapha
Addini

Abin da ya sa Hukumar Tace Finafinai take gudanar da taron Mauludi – El-Mustapha

November 29, 2025
Surar yaƙin jihadin Islama (Hoto daga shafin History of Islamic Wars, a Facebook)
Addini

Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka: Daga Wali Ɗanmasani zuwa jiya

June 21, 2023
Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi
Addini

Baban mu Shehu Ɗahiru Bauchi ya cika shekara 98

August 2, 2022
Sheikh Ibrahim Khalil
Addini

Majalisar Malamai: Har yanzu Sheikh Ibrahim Khalil ne shugaba, inji gamayyar malaman Kano

October 12, 2021
Sheikh Ibrahim Khalil
Addini

Malamai sun bayyana tsige Sheikh Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malaman Kano

October 11, 2021
Hukuncin ranar Idi
Addini

Hukuncin ranar Idi

May 12, 2021
Next Post
Ƙungiyar ‘yan fim ta Matan Mu A Yau ta yi taron farfaɗowa

Ƙungiyar 'yan fim ta Matan Mu A Yau ta yi taron farfaɗowa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!