• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙungiyar ‘yan fim ta Matan Mu A Yau ta yi taron farfaɗowa

by Editors
September 24, 2025
in Uncategorized
0
Ƙungiyar ‘yan fim ta Matan Mu A Yau ta yi taron farfaɗowa

Membobin ƙungiyar Matan Mu A Yau bayan sun kammala taron su

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WATA ƙungiyar mata ‘yan fim mai suna Matan Mu A Yau ta yi taron masu ruwa da tsaki na ƙungiyar domin tsara yadda za su farfaɗo da ita tare ci gaba da ayyukan da suke yi tun tsawon shekarun da aka kafa ta.

An yi taron a gidan ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar, wato Hajiya Hauwa ‘Yargwana da ke unguwar Gaida a birnin Kano.

Tun da farko dai take bayani a kan manufar taron, Shugabar ƙungiyar, Hajiya Zulai Bebeji, ta ce: “Manufar kiran wannan taron shi ne don mu haɗu mu tattauna a game da tafiyar da ƙungiyar da kuma dawo da martabar ta.

“Domin kuwa abu ne da kowa ya sani kusan shekaru bakwai da kafa wannan ƙungiyar, mun yi abubuwa da dama na tallafa wa mutane da kuma taimakon junan mu. To amma a yanzu muke ganin mun ɗan yi sanyi, don haka ya kamata mu samo bakin zaren.”

Ta ƙara da cewa: “Ita manufar wannan ƙungiyar ba wai ta tsaya ga ‘yan fim ba ne, duk wata mace da take da buƙatar a haɗu a taimaki juna kuma a taimaki waɗanda suke buƙatar taimako, to muna maraba da ita.

“Amma dai mafi yawan mu da muke cikin ƙungiyar, jaruman fim ne, sai dai mata ‘yan siyasa da masu gudanar da harkar kasuwanci da ma’aikatan gwamnati duk a tafiyar.

“Sanin kowa ne a baya mun yi abubuwa da dama na taimakon junan mu kamar lokacin bikin aure ko haihuwa ko rashin lafiya ko suna. Duk waɗannan abubuwan an yi wa mutane kuma sun ji daɗi.

“To a yanzu ya za a yi mu ci gaba da wannan abubuwan alheri da ma wasu a nan gaba? Dole ne sai mun samar da mafita da tsara yadda za mu tafiyar da abin, don haka muka kira taron.

“Muna fatan wannan zama namu zai samar mana da hanyoyin da ƙungiyar mu ta Matan Mu A Yau za ta samu cigaban da za mu daɗe muna cin moriyar sa har zuwa ‘ya’yan mu da jikoki.”

A taron dai an tattauna muhimman abubuwa tare da bayar da shawarwari.

Haka nan an samar da hanyoyin da ƙungiyar za ta rinƙa samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan ta ba tare da ana cewa a kawo a harhaɗa daga wajen ‘yan ƙungiya ba.

Cikin hanyar da aka samar akwai yunƙuri na shirya fim a ƙarƙashin ƙungiyar wanda ƙungiyar za ta nemi haɗin gwiwa da wasu ƙungiyoyi ko kamfanoni don samar da kuɗin da za a yi fim ɗin.

Wasu daga cikin jaruman da suka halarci wajen akwai shugabar ƙungiyar, Hajiya Zulai Bebeji, da Hajiya Bilkisu Maigado, jaruma a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’, Ruƙayya Sharaɗa, jaruma a cikin shirin ‘Garwashi, da sauran su.

Loading

Previous Post

Mauludi: Duk da ruwan sama ya hana, na ga taron masoya Annabi – Sayyada Raihan Imam Kamshi

Next Post

Jaruma Rasheeda Maisa’a ta samu muƙami a Gwamnatin Tarayya

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Sani Danja: Waƙar ‘Barau Jigijim’ ta tayar da ƙura, ya ƙaddamar da gasa a kan ta
Mawaƙa

Sani Danja: Waƙar ‘Barau Jigijim’ ta tayar da ƙura, ya ƙaddamar da gasa a kan ta

July 15, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Next Post
Jaruma Rasheeda Maisa’a ta samu muƙami a Gwamnatin Tarayya

Jaruma Rasheeda Maisa'a ta samu muƙami a Gwamnatin Tarayya

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!