Rasheeda Adamu Abdullahi (Maisa’a) ita ma ta bi sahun jaruman Kannywood da suke samun muƙami a Gwamnatin Tarayya, inda aka naɗa ta a matsayin mataimakiya ta musamman ga mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin mabuƙata ta musamman da samar da daidaito ga ‘yan ƙasa a ƙarƙashin ofishin Muhammad Abba Isa.
Haka kuma jarumar ta samu wani muƙamin a ƙungiyar Uwargidan Shugaban Kasa Remi Tinubu, wato “Remi Tinubu Support Organisation” inda aka naɗa ta mai kula da jihohin Arewa-maso-yamma, kamar yadda takardar mai ɗauke da kwanan wata 25 ga Agusta ta tabbatar.

Rasheeda dai tana cikin ‘yan fim da suke shiga harkar siyasa, domin ko a zamanin Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a karo na farko an ba ta muƙamin mataimakiya a kan harkokin mata.
![]()







