FITACCEN marubucin littattafan Hausa kuma malami a Kwalejin Gwamnatin Tarayya dake Kano, Kamilu Ɗahiru Gwammaja, ya samu nasarar kammala digirin sa na uku.
Malam Kamilu ya gabatar da nazarin sa a kan yalwar ma’ana ta hanyar tsokaci daga wasu maganganu na marigayi Malam Aminu Kano, kuma hakan ne ya kai shi ga kaiwa matakin nasarar kammala digirin nasa.
Gwammaja yana cikin marubuta tun ana rubutun labarin soyayya, daga baya kuma ya koma yin rubutun littattafai na ilimi, inda a nan ma ya rubuta masu yawa.
Ɗaya daga cikin sanannun littattafan sa shi ne Tsanin Hausa, na 1 zuwa n 6, da kuma Jagoran Nazarin Karin Magana.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a soshiyal midiya a yau Alhamis, Dakta Kamilu Ɗahiru Gwammaja ya ce: “Na samu amincewar malamai na na samun shaidar PhD, wato Dr, a nazarin harshen Hausa. Godiya ga jagoran gudanar da binciken, Farfesa Isa Mukhtar, da jagoran duba binciken na gida, Farfesa Usman Usaini Fagge, da Shugaban Sashe, Dr Jibril Shu’aibu Adamu, da jagorar kula da manyan ɗalibai, Farfesa Halima Abdulƙadir Ɗangambo, da mai kula da gabatar da muƙaloli, Dr Muhammad Sulaiman Abdullahi, da dukkanin malaman Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na Jami’ar Bayero ta Kano da jagoran duba bincike na waje da zaman sahalewa, Farfesa Salisu Garba daga jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Allah ya saka wa kowa da alheri. Dr Kamilu Dahiru Gwammaja.”

Jama’a da dama sun aika wa malamin da murnar samun wannan babbar nasara da ya yi.
![]()







