MASU shirya Ranar Marubuta ta a Duniya ta bana sun yi nisa wajen shirye-shiryen bukin wanda ake sa ran zai gudana a Dutse, Jihar Jigawa, daga ranar 31 ga Disamba, 2025 zuwa 1 ga Janairu, 2026.
Daga cikin tsare-tsaren bukin, wanda za a gabatar a Dutse, Jihar Jigawa, an shirya gasar rubutun gajerun labaran Hausa a kan batun Fasahar Zamani, wato Artificial Intelligence (AI) da batun tsaro domin ta dace da taken taron na bana, wato “Marubuta a Ƙarni na 21: Ƙalubalen Tsaro da Tattalin Arziki”.
Gasa ce wadda take a buɗe ga dukkan masu sha’awar shiga daga marubuta maza da mata sanannu da sababbi da ma masu sha’awar fara rubutu matuƙar za su kiyaye ƙa’idojin gasar.
Cikin wata sanarwa da aka saki a soshiyal midiya, Dakta Mujaheed Abdullahi Kudan ya bayyana manufofin gasar a madadin kwamitin shirya ta kamar haka:
1. Ƙarfafa marubuta su yi nazari kan yadda fasahar AI (Artificial Intelligence) ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro da kuma bunƙasa tattalin arziki.
2. Samar da sababbin ra’ayoyi da mafita na zamani da za su iya taimaka wa al’umma wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da tattalin arziki.
3. Gina wata hanya ta tattaunawa da musayar ra’ayi kan amfanin fasahar zamani a cigaban ƙasa.
4. Ba wa marubuta damar nuna fasaha da basira da ƙwarewar su a fannin rubutu da bincike ko ƙirƙira.
5. Haɗa marubuta da masu amfani da fasahar zamani domin a samu haɗin gwiwa wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arziki.
6. Ƙarin samar da abin karatu mai inganci da manufa cikin harshen Hausa.
Haka kuma ya lissafa tsare-tsaren shiga gasar kamar haka:
1. Za a aika da samfurin labarin da za a rubuta cikin kalmomin da ba su gaza 500 ba kuma ba su wuce 800 ba, ta wannan adireshin: ranarmarubutanhausa2025@gmail.com daga ranar 21/09/2025 zuwa ranar 21/10/2024.
2. Za a tace a zaɓi 30 cikin samfurin labaran da aka tura waɗanda suka fi burgewa a cikin kwanaki goma (21/10/2025 zuwa 31/10/2025).
3. Za a yi bita ta musamman ga masu waɗannan samfurin labaran 20 a kan fasahar AI da tsaro da tattalin arziki da kuma rubutun gajerun labarai (musamman saboda sababbin marubuta).
4. Bayan bitar, za a buƙaci kowannen su ya rubuta cikakken labarin sa wanda bai gaza kalmomi 1,000 ba kuma bai wuce kalmomi 1,500 ba bayan bitar, daga 15/11/2025 zuwa 15/12/2025.
5. Za a bayyana labaran da suka yi nasara a wajen bukin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya 2025.
Bugu da ƙari, Dakta Kudan ya jera sharuɗɗan shiga gasar kamar haka:
1. A tabbatar rubutun ya dace da batutuwan da suka shafi fasahar AI, musamman dangane da tsaro da tattalin arziki.
2. A tabbatar an yi amfani da daidaitacciyar Hausa kuma an kiyaye ƙa’idojin rubutun Hausa. Sannan dole ne a yi amfani da haruffa masu lanƙwasa (wato ɓ, ɗ, ƙ, ‘y).
3. A tabbatar an aika da rubutun a tsarin Microsoft Word ko PDF zuwa ga wannan email ɗin: ranarmarubutanhausa2025@gmail.com. tare da shaidar yin rajista.
4. A tabbatar ba a taɓa shiga wata gasa da labarin da za a tura ba, kuma ba a taɓa buga shi a jarida ko wata kafa ko zaurukan soshiyal midiya ba.
5. Wanda ya yi rajista da taron Ranar Marubuta Hausa kaɗai ne zai iya shiga gasar.
6. Mutane biyu za su iya shiga gasar da labari ɗaya. Kuma dole ne a aika da labari cikin lokacin da aka ƙayyade.
7. Kada labarin ya zamto ya ci zarafi ko tozarta wata al’umma ko ɗaiɗaikun mutane.
7. Ba a yarda a sake ɗaukar duk labarin da aka shiga da shi gasar a sake shiga wata gasar da shi ba.
8. A sani, hukunci da sakamakon alƙalan gasar shi ne na ƙarshe, ba za a sake tattauna shi ba a wani waje.
9. Kowane marubuci na iya shiga gasar ban da membobin kwamitin ƙoli na shirya taron.
Sanarwar ta zayyana irin kyaututtukan da za a ci a gasar, kamar haka:
1. Za a bayar da kyaututtuka ga labarai uku da suka yi zarra a matakin na 1 zuwa na 3.
2. Za a bayar da takardar shaidar karramawa da awalajar littattafai ga waɗanda suka shiga gasar daga na 1 zuwa na 15, kuma za a duba yiwuwar buga labaran nasu cikin littafin da za a ƙaddamar da shi a taron shekara mai zuwa ta 2026.
![]()







