Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta bayyana cewa tana da ikon sa ido kan waƙoƙi da tarurrukan sha’irai a jihar.
Ta faɗi haka ne a cikin martanin da ta yi wa wani lauya a Kano mai suna Abba Hikima, wanda ya yi tsokaci game da ikon doka da hukumar take da shi kan sha’irai.
Kamar yadda mujallar Fim ta ruwaito, lauyan ya bayyana cewa hukumar ba ta da hurumin doka wajen saka baki a muhawarar da ke tsakanin wasu sha’irai biyu, wato Shehi Mai Tajul’izzi da Usman Maidubun Isa.
Sai dai hukumar, a wata sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 20 ga Satumba, 2025, wadda Jami’in Yaɗa Labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya sanya wa hannu, hukumar ta bayyana cewa wannan matsayi da Hikima ya ɗauka ba daidai ba ne kuma yana nuna kuskuren fahimta kan dokokin da suka kafa hukumar.
Hukumar ta ce, “Dukkan su Shehi Mai Tajul’izzi da Usman Maidubun Isa sha’irai ne da doka ta saka su a ƙarƙashin kulawa da duba aikace-aikacen su gare mu.”
Ta ce asalin abin da ya haifar da muhawarar da ta shiga tsakanin su ta samo asali ne daga kalaman waƙoƙin su, wanda hakan ya sanya lamarin cikin ikon hukumar bisa tsarin dokar ta.
A cewar ta, dokar kafa hukumar ta bai wa hukumar ikon da ya haɗa da yin rajista da bayar da lasisi ga sha’irai; kula da abin da suke fitarwa (wato waƙoƙin su) da sa ido kan ayyukan su a bainar jama’a, wato yayin majalisi; tabbatar da bin doka da oda, ciki har da bincike, hukunta masu karya doka, ko dakatar da lasisin su idan ya zama dole.
“Saboda haka, hukumar tana da cikakken ikon doka wajen saka baki a irin wannan lamari, don kare zaman lafiya, tarbiyya da martabar ɓangaren masu yabon Manzon Allah (S.A.W.),” inji jami’in.
Ya ƙara da cewa, “Muna girmama ra’ayoyin masana a ɓangaren shari’a, tare da jan hankalin su kan cewa irin wannan kuskuren fassara daga masu ilmin doka, musamman waɗanda suka san tsarin doka irin shi Abba Hikima, na iya rage darajar hukumomin gwamnati.”
Hukumar ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ci gaba da yin aiki cikin lumana da bin dokar hukumar kamar yadda ya kamata.
Hakan dai ya biyo bayan wani zama ne da ta kira mawaƙan biyu kan taron muƙabalar da suka yi a tsakanin su inda aka tashi baram-baram da neman tayar da hayaniya.
Shehi Tajul izzi ya je da lauyan sa, Abba Hikima, yayin da Usman Mai Dubun Isa bai samu zuwa ba, sai wakilci ya tura.
Bayan zaman ne Abba Hikima ya bayyana cewa hukumar ba ta da hurumin gayyatar mawaƙan a kan muƙabalar da suka yi.
![]()







