
Jami’a mai suna European American University da ke ƙasar Panama ta karrama mawaƙi Dauda Adamu Kakutu (Rarara) da “digirin digirgir,” wato Dakta, a yau a Abuja.
An ce an ba shi digirin ne saboda tallata al’adu da zaburar da matasa da yake yi a Nijeriya.
A gagarumin taron, manyan mutane irin ‘yan siyasa da sauran masoya Rarara masu yawan gaske sun halarta.

Bai wa Rarara wannan “digiri” ya haifar da ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya, inda yayin da masoyan sa suna taya shi murna, wasu kuma suna ɗora ayar tambaya a kan ita darajar jami’ar da dalilin bada digirin.
Kamar yadda mujallar Fim ta ruwaito a jiya, ba Rarara ba ne mawaƙi na farko da wata jami’a ta ba digirin karramawa na dakta, domin kuwa an taɓa ba Aminu Ala da Nura M. Inuwa a mawaƙan zamani, can a baya kuma an ba Shata da Ɗanmaraya Jos.
Jami’ar da digirin duk na bogi ne
Bayan mun buga wannan labarin, hujjoji sun bulla cewa digirin da aka ba Rarara na bogi ne. Ita kan ta jami’ar ta bogi ce.

![]()







