MAWAƘI a Kannywood, Malam Muddassir Ƙasim, ya na kira ga ‘yan Nijeriya da su yi aiki da hankali wajen zaɓen shugabannin su a zaɓuɓɓukan da za a yi a bana.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tsara gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya a ranar Asabar mai zuwa, 25 ga Fabrairu, sannan a yi na gwamnoni da Majalisun Jihohi a ranar 11 ga Maris.
A yayin da kowa ya ke tofa albarkacin bakin sa a kan lamarin, Malam Muddassir ya wallafa wani saƙo a Facebook inda ya faɗakar da jama’a kan abin da ya kamata su yi.
Ya ce: “Zaɓen bana akwai rikitarwa a ciki, akwai ruɗu a ciki, kowa sai ya yi aiki da hankali.
“Kar fushi ya sa garin canjin takalmi ka taka ƙaya. Kar ka yarda a ce ka zaɓi wane, haka kuma kar ka yarda a ce kar ka zaɓi wane.
“Natsu ka yi amfani da hankalinka da ra’ayin ka, in ba ka da ra’ayin kan ka, to a gamsar da kai hujjojin da za su sa ka zaɓa ko kar ka zaɓa.
“In ba ka gamsu da hujjojin ba, to tambayi me Allah da Manzo (su ka) ce a kan tsai da shugaba, ka yi don Allah ka bar wa Allah ikon shi.”