• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kotu ta umarci a maida su Murja Kunya kurkuku

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
February 24, 2023
in Labarai
0
Murja Ibrahim Kunya

Murja Ibrahim Kunya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WATA kotu a Kano da ke yin shari’a bisa tuhumar jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya da wasu mutum uku da aikata baɗala a jiya ta ba da umarnin a mayar da su gidan yari inda ake tsare da su.

Mutum ukun su ne Ashir Idris (Maiwushirya), Aminu BBC da mawaƙi Sadiq Shehu Shariff.

Idan kun tuna, a ranar 16 ga Fabrairu, 2023 mujallar Fim ta ruwaito labarin yadda ‘yan sanda sun kama mutanen tare da gurfanar da su a gaban kotun a bisa tuhumar su da kalaman batsa da ɓata tarbiyya. Amma sun musanta zargin.

Tun da fari, wata ƙungiya mai suna Zauren Malaman Kano ce ta kai kukan matasan ga ‘yan sanda.

A zaman da aka yi jiya Alhamis, 23 ga Fabrairu, an kara karanto wa su Ashir Maiwushirya da sauran biyun da ake tuhuma laifin su kamar yadda lauyan su, Barista Mustapha Alimi, ya buƙata.

Lauyan ya nemi kotun da ta ba da dama a ƙara karanto masu laifin su domin su na buƙatar su sauya musantawa zuwa amsa laifi, kuma nan take kotu ta bayar da damar. Bayan an karanto masu ɗin sai kuma nan take su ka amsa laifin.

Ita kuwa Murja, lauyoyin ta sun sanar wa kotu da cewa sun samu daidaito da lauyoyi masu gabatar da ƙara, inda kuma kotun ta tambayi lauya mai gabatar da ƙara, Barista Lamiɗo Soron Ɗinki ko sun yi hakan? Sai ya amsa da cewa haka ne, kuma ya buƙaci kotun da ta ba shi damar ya koma ofishin lauyan Murja domin ya karɓo takardar saboda a zaman da su ka yi ba a sanya wa takardar hannu ba.

Kotu ta amince da roƙon nasa. 

Shi kuma lauyan Murja, Barista A.D. Saka, ya nemi kotu da ta ba da belin wadda ake ƙara. 

Alƙali ya ce ai da man tun a baya an yi magana kan roƙon beli.

A nan ne aka samu wata cacar baki tsakanin lauyan Murja da na gwamnati, har ta kai ga an tafi hutu.

Ana shirin dawowa ne kuma sai aka samu labarin cewa garin ya na cikin wani yanayi na rashin tsaro saboda artabun siyasa tsakanin ‘yan Kwankwasiyya da ‘yan Gandujiyya, don haka sai aka ɗage zaman shari’ar zuwa ranar 2 ga Maris.

Kotu ta sake aikawa da su Murja gidan yari har zuwa ranar da za a koma domin ci gaba da shari’ar.

Loading

Tags: Aminu BBCAshir MaiwushiryaKanokotuMurja Ibrahim KunyaSadiq Shehu Shariffshari'aTikTokZauren Malaman Kano
Previous Post

Mawaƙin Kannywood Muddassir Ƙasim ya ja hankalin masu zaɓe kan abin da ya dace

Next Post

Faɗar sunan Nazifi Asnanic cikin ‘yan tarzoma ya tada hankalin mawaƙin Kannywood

Related Posts

AFMAN ta taya Sarari murnar samun damar halartar taron baje-kolin finafinan Nijeriya a Toronto da fim ɗin ‘Kakanda’
Labarai

AFMAN ta taya Sarari murnar samun damar halartar taron baje-kolin finafinan Nijeriya a Toronto da fim ɗin ‘Kakanda’

June 16, 2025
Naɗa ni jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder da aka yi zai amfani Kannywood baki ɗaya, inji furodusa Abubakar Galadima
Labarai

Naɗa ni jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder da aka yi zai amfani Kannywood baki ɗaya, inji furodusa Abubakar Galadima

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
Next Post
Nazifi Asnanic

Faɗar sunan Nazifi Asnanic cikin 'yan tarzoma ya tada hankalin mawaƙin Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!