MAWAƘIN Manzon Allah, Malam Abdullahi Ɗan Gano, ya rasu a shekaranjiya Asabar sakamakon wani mummunan haɗarin mota da ya yi a ranar Laraba da ta gabata a hanyar Maiduguri.
Haɗarin da ya auku da yammacin ranar lokacin da marigayin yake kan hanyar sa ta komawa daga Kano zuwa garin su Gano da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu inda motar da yake ciki ta ƙwace ta daki babbar motar da ke gaban ta.
Sakamakon haɗarin, Malam Abdullahi ya samu karaya guda uku a hannu da ƙafa.
Bayan an kai shi asibiti da kwana uku Allah ya yi masa rasuwa.
An yi jana’izar sa a jiya Lahadi a gidan sa da ke garin Gano.


Marigayin mai kimanin shekaru 42 ya rasu ya bar matar sa da ‘ya’ya biyar.
Yana ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan yabon Manzon Allah (SAW) a tsawon lokaci, inda ya yi waƙoƙin yabon Annabi masu yawan gaske.
Waƙar sa da ta fi yin fice ita ce waƙar “Saba’a.”
Allah ya jiƙan sa, amin.