MAWAƘIYA a Kannywood, Hajiya Jamila M. Muhammad, wadda aka fi sani da Jamila Kogi, za ta yi saukar Alƙur’ani mai tsarki a watan gobe.
Za a gudanar da taron saukar a safiyar ranar Asabar, 21 ga Oktoba, 2023 a ɗakin taro na Sultan Bello da ke Unguwar Sarkin Musulmi a garin Kaduna.

Za ta yi saukar ne a ƙarƙashin makarantar su ta Islamiyya mai suna ‘Zubairu Usman College of Islamic and Arabic Studies’ da ke lamba 12, Range Close, Shooting Range, Kabalan Doki, Kaduna.
Mawaƙiyar, wadda ke zaune a garin Kaduna, ta ce ta na gayyatar dukkan ‘yan’uwa da abokan arziki, to amma duk wanda bai samu damar halarta ba ya taya ta da addu’a.