A RANAR 5 ga Yuli, 2024 aka ɗaura auren mawaƙiya a Kannywood, Zainab A. Baba, a Kano.
Mujallar Fim ba ta samu sunan wanda ta aura ko wani ƙarin bayani ba. Ba a yi gagarumin biki irin wanda wasu ‘yan fim ke yi ba, kuma da alama ba a so a san wanda zabiyar ta aura.
Wasu daga cikin ‘yan fim sun je gidan su Zainab ɗin domin taya ta murna. Sun haɗa da mawaƙa Fati Nijar da Hadiza Maikano.
Zainab ƙanwa ce shaƙiƙiya ga fitacciyar mawaƙiya Maryam A. Baba, wadda ta jima da yin aure.
Allah ya ba da zaman lafiya da ƙaruwar arziki, amin
Ga wasu hotuna daga bikin.






