MINISTAN Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya bayar da shawarar tallafa wa ƙungiyoyin ƙasashen duniya da masu ruwa da tsaki na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC) domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da Manajan Daraktan Hukumar Shirya Finafinan, Alhaji Ali Nuhu, da manyan jami’an hukumar su ka kai masa ziyarar aiki a ma’aikatar, a ranar Alhamis a Abuja.
Bagudu ya yi nuni da cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gangan ya kafa Ma’aikatar Al’adu da Ƙirƙire-ƙirƙire domin ya fahimci cewa wasu ƙungiyoyi ko fannonin ayyuka na taimakawa wajen bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce, “Babbar kadarar mu ita ce Masana’antar Ƙirƙire-ƙirƙire kuma ta kasance babbar ma’aikatar samar da aikin yi.”

Don haka ya yi kira ga manajan daraktan na NFC da ya samar da damarmaki masu kyau ga matasa domin cin gajiyar wannan sana’a.
Bagudu ya kuma shawarci hukumar da ta nemi haɗin gwiwa da KOICA ta ƙasar Koriya ta Kudu, Japan da Ofishin Jakadancin Faransa, don ciyar da masana’antar ƙirƙire-ƙirƙire ta ƙasar nan gaba.
Ministan ya yi kira ga Ali Nuhu da ya kawo cigaba cikin gwamnati, ya yi amfani da basirar sa ta ƙirƙire-ƙirƙire wajen isar da saƙonni masu kyau na ‘Renewed Hope’ da kuma aiwatar da aiki ga ‘yan Nijeriya.
Da yake nasa jawabi, Ali Nuhu ya ce: “Manufar ƙara yawan kuɗaɗen da ake warewa a kasafin kuɗin hukumar, ba ta damar cimma ayyukan ta ne.”
Haka kuma ya yi nuni da cewa ƙaruwar ƙarin kasafin kuɗi zai bai wa hukumar damar kula da ofisoshin hulɗa da jama’a da bunƙasa wurin zaman hukumar na dindindin da ƙara ƙarfin ma’aikatan da ake da su da kuma ɗaukar ma’aikata aiki.

Ita ma Daraktar Cigaban Tattalin Arziki, Misis Elizabeth Egharevba, ta ce, “Masana’antar nishaɗin mu ta na ba da gudunmawa ga cigaban tattalin arzikin mu, kuma naɗa ku da shugaban ƙasa ya yi, mu na da tabbacin za ku sami ƙarin nasara.”
NFC dai tana ɗaya daga cikin masu fafutika a Ma’aikatar Al’adu da Tattalin Arziki ta Tarayya kuma ta na da hurumin bunƙasa masana’antar finafinai da al’adun finafinai a Nijeriya.