• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, July 24, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Minista Sadiya ta ƙaddamar da shirin N-Power kashi na uku

by DAGA WAKILIN MU
August 24, 2021
in Nijeriya
0
Minista Sadiya ta ƙaddamar da shirin N-Power kashi na uku
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAR Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ƙaddamar da shirin nan na bai wa matasa tallafin fara sana’a mai suna N-Power.

Mutum 510 aka ɗauka a wannan matakin shirin a jihohi 36 da Gundumar Birnin Tarayya (FCT).

Lokacin da ta ke ƙaddamar da zangon ‘C’ na shirin, wato ‘Batch C’ a ranar Litinin a ɗakin taro na NAF Conference Centre da ke Abuja, Hajiya Sadiya ta taya masu cin moriyar shirin da su ka yi nasarar shiga wannan matakin waɗanda aka ɗauka murna, sannan ta shawarce su da su yi amfani da wannan damar da aka ba su.

Ministar ta yi la’akari da cewa an yi wasu sauye-sauye a tsarin zaɓen masu cin moriyar N-Power kuma ta sha alwashin cewa ma’aikatar ta ta ƙudiri aniyar tabbatar da cewa za a cimma dukkan manyan muradan da aka tsara na shirye-shiryen inganta rayuwa na tarayya (National Social Investment Programmes).

Ta ce, “An shigo da wasu sababbin dabaru cikin zaɓen ‘yan shirin N-Power da hanyar biyan su kuɗi wanda ya haɗa da ƙirƙiro tsarin gudanar da harkar inganta rayuwa na ƙasa, wato ‘National Social Investment Management Systems’ (NASIMS), haɗin gwiwa da manyan hukumomin gwamnati irin su NYSC, UBEC, NPHCDA, NOA da wasu masu yawa, waɗanda tare da su ne ma’aikatar mu ke tafiya sosai don aiwatar da shirye-shiryen ta.

“Don tabbatar da magance matsalar sadarwa, dangane da takurar tafiyar saƙwanni, faɗaɗar intanet a ƙasar nan, wannan ma’aikatar ta samar da hanyar samun bayanai ta manhajar USSD. Taƙaitacciyar kalmar USSD ɗin, wato *45665# ita ce za ta bayar da haɗin intanet da mutum ke buƙata da kuma tallafin jami’an kimiyya don samun isa ga ayyukan bada bayanai ga masu cin moriyar shirin mu.”

Ministar ta gode wa Shugaba  Muhammadu Buhari saboda hoɓɓasan da gwamnatin sa ke yi wajen kawar da fatara a ƙasar nan tare da ci gaba da   Shirye-shiryen Inganta Rayuwa na Ƙasa (NSIPs). 

Ta kuma gode wa membobin Majalisar Tarayya saboda yadda su ka amince a kashe kuɗaɗe kan shirin na N-Power tare da aikin sa ido da su ke yi don tabbatar da cewa ana aiwatar da shirin kamar yadda aka tsara.

Minista Sadiya ta raba takardun kama aiki ga wasu daga cikin waɗanda su ka samu nasarar shiga shirin.

Ƙaramar Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Ambasada Mariam Yalwaji Katagum, da Ministar Harkokin Mata, Uwargida Pauline Tallen, da Rasdan kuma babban Kodinetan Harkokin Agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Edward Kallon,  tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Amayanabo na Twon-Brass a Jihar Bayelsa, Alfred Diette Spiff, da sauran manyan mutane su na daga cikin waɗanda su ka yi jawaban sa alheri a wajen taron.

Fitaccen mawaƙin nan mai suna D’banj kuma ya nishaɗantar da mahalarta taron.

Shi dai zangon ‘Batch  C’ na shirin N-Power, an raba shi ne zuwa matakai biyu. Matakin C1 ya ƙunshi masu cin moriyar shirin mutum 510,000 yayin da matakinwhile stream C2 ya ƙunshi mutum 490,000. 

A ƙarƙashin Batch C1, an zaɓi jimillar mutum 450,000 don su amfana a ƙarƙashin sashen waɗanda su ka kammala karatun jami’a, sai mutum 60,000 marasa digiri.

Shirin N-Power, wanda ya ɗora fifiko kan Aikin Gona, Kiwon Lafiya  harkar Konfuta da Intanet (ICT), Kasuwanci da Gine-Gine, ana shigar sa ne ta hanyar cike fom a intanet da kuma tsarin zaɓar masu cin moriya don a tabbatar da adalci ga kowa, tare da tsare gaskiya da inganci wajen ɗaukar masu cin gajiyar sa.

Loading

Tags: Batch C of N-PowerDisaster Management and Social DevelopmentMinistry of Humanitarian AffairsN-PowerNational Social Investment ProgrammesPoverty AlleviationSadiya Umar Farouq
Previous Post

‘Yan Kannywood sun yi tir da kalaman Ummah Shehu

Next Post

Yadda Adam Zango ya so ya auri Ummi Rahab – Yasir Ahmad

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Yadda Adam Zango ya so ya auri Ummi Rahab – Yasir Ahmad

Yadda Adam Zango ya so ya auri Ummi Rahab - Yasir Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!