MATASHIN nan da ake cewa shi ne ya ɗaure wa Ummi Rahab gindi har ta yi wa Adam A. Zango barazanar za ta tona masa asiri ya maida kakkausan martani kan maganganun da ake yaɗawa. A ciki, ya ƙaryata Zango a kan iƙirarin wai bai taɓa yin soyayya da jarumar ba, da kuma batun wai ya rabu da ita ne saboda ba ta yi masa biyayya.
Matashin, mai suna wato Yasir M. Ahmad, wanda ya ce shi ɗan’uwa ne ga jarumar, ya yi magana kan batun cewa Rahab ta butulce wa Zango bayan ya ɗaga tauraruwar ta a Kannywood, da kuma batun wai ba ta da iyaye.
Ta cikin wani saƙon bidiyo da ya fitar a yau a Instagram mai tsawon minti 20, Yasir ya bayyana cewa faro labarin sa da cewa shi ne silar shigar Rahab harkar fim, ba Zango ba.
A bidiyon, wanda wakilin mujallar Fim ya kalla a tsanake Yasir ya ce, “Na farko dai, Adamu ba shi ya kawo Ummi industiri ba, kuma Adamu ba shi da alaƙa ta ‘family’ ko wani dangi ko na nesa ko na kusa. Hasali ma sun haɗu a fim ɗin ‘Ummi’ ne; ta zo ne, shi ma ya zo, don a lokacin ba zan taɓa mantawa ba fim ɗin ‘Ummi’ ma kamar lokacin za mu yi tafiya ne sai Mu’azzamu Idi Yari, a lokacin ya zo gurin mu ni da yarinyar nan, ya ce don Allah ya na so ta yi masa aikin nan, don a lokacin tafiya za mu yi, za mu je biki ne.
“To, sai Umar Kanu, mijin Fati Muhammad, shi ne ya ba shi lambar mu ya zo ya same mu har tasha, ya nemi wannan alfarmar, aka zo aka yi wannan fim ɗin, ‘Ummi’.
“A nan mu ka fara ganin Adamu, ita ma a nan ta fara ganin shi, don a lokacin ya yi aiki da yarinyar a fim ɗin ‘Ummi’, ya ga masha Allah ta yi aiki mai kyau, wanda a lokacin wannan fim ɗin ta fara yi.
“To, bayan an gama aikin ne kuma mu ka yi musayar lambobin waya. To wannan dai shi ne haɗuwar mu ta farko da Adamu.”
Ya ƙara da cewa fim ɗin ma da jarumar ta fito ba na Zango ɗin ba ne, na Mu’azzamu idi Yari ne, shi ne darakta da kuma furodusa Abdul Amart.

Yasir ya ci gaba da faɗin, “Bayan sati biyu, a lokacin sai na ga wayar Adamu ya kirawo ni. Ya na ce min yarinyar nan sun saba da ɗan sa Haidar, ya ce don Allah ya na neman alfarma idan dai ta samu hutu ya na so ta zo gidan sa ta yi hutu, don a lokacin ma ta na zuwa makaranta. To bayan sun yi hutu, kamar yadda aka yi alƙawari, ni da kai na na je har Kaduna na kai masa yarinyar nan. A can na bar ta. Bayan sati biyu har wa yau sai ya dawo da ita gida.”
Yasir ya kuma ƙaryata raɗe-raɗin da ake yi na cewar Rahab ba ta da iyaye, ya ce ba haka ba ne.
“Maganar da ake yi na cewar Ummi ba ta da mahaifiya ko mahaifi, maganar ba haka ta ke ba. Hasali ma akwai lokacin da Adamu ya shirya za shi Saudiyya, ya zo ya karɓi lambar mahaifiyar yarinyar nan a lokacin, ya ce mani idan sun je Saudiyya za su gaisa. Na ɗauka na ba shi, su ka je Saudiyya da shi da Afakallahu da Rarara, su ka je.
“Bayan sun yi aikin su na Umara su ka kirawo ta a waya, don a lokacin ma ita ta zo ta same su a masaukin su, su ka yi magana. A lokacin ma har ya nuna sha’awar ya na so ya aure ta. Kuma babar ta a lokacin ma ta kira ni ta yi mani bayanin abin da ya faru.”
Ya ce lallai a lokacin akwai soyayya tsakanin jarumin da jarumar, don Zango ya nuna ya na ƙaunar ta.
Ya ce, “Don ni ma wannan abin na kula da shi, shi ya sa a lokacin ba na iya yin wani abu, don na san a lokacin akwai ƙauna.
“Akwai lokacin da Ali Nuhu ya kira ni a lokacin ina tare da ita, ya ce min, ‘Yasir ne?’ Na ce, ‘E.’ Sai ya ce don Allah ya na so za su yi aiki da wannan yarinyar Ummi, wani aiki ‘Labiba’; zai tura min sikirif a Kaduna. Na ce masa ba matsala.
“A lokacin kuma ta yi finafinai dai kamar guda biyar ne ko shida ne, irin ta yi ‘Labiba’, ta yi ‘Sadakar Yalla’, ta yi ‘Watan Wata Rana’, irin su ‘Gudan Jini’. To a lokacin wannan finafinan su ne wanda ta yi kuma a lokacin duk waɗannan finafinan ba su fito ba.

A lokacin, Adamu bayan ta dawo hutu ya ƙara neman don Allah yarinyar nan za ta ƙara zuwa hutu gidan sa ta ƙara yin hutun makaranta idan an yi saboda dai ‘ya’yan sa. To, ta yi dai wannan hutu da ya nemi alfarma. Kuma dai ni na ɗauki yarinyar nan na ƙara kai ta, da kai na na kai ta har gidan sa. A lokacin ma ba ya nan, sai mu ka yi waya da shi. Na tafi na bar ta wurin matan sa.
Yasir ya ci gaba da cewa, ”Bayan kwana biyu, na dawo Kano sai na samu labarin (Zango) ya rabu da matan sa, an ɗauki yarinya an kai ta wajen mahaifiyar sa, ta na zaune a gurin ta. Bayan a lokacin ni kuma ina cikin ‘yan’uwa, ina ta shan tambayoyi, ‘Ina Ummi? Ina Ummi?’
“Don a lokacin ban samu lokaci ba ne, da na dawo na ɗauke ta, amma in-sha Allahu zan zo na ɗauke ta. Kuma a lokacin ma akwai yaya na da bai ma samu labarin Ummi ta na wani fim ba. Ni ban ɗauki fim komai ba, na ɗauka da man fim a guri na sana’a ce, shi ta ke yi.
“To amma sai ya ce, ‘Da man yarinyar nan fim ta ke yi?’ Ya ga sunan Ummi na ya fito, don ni ko gaya masa ban yi ba saboda a lokacin mu na tare da ita yarinyar Ummi To, yayan nawa da ya zo ya fara gaggaya min maganganu.
“To, amma a lokacin ka san ita rashin fahimta; daga baya kuma da ya fahimci cewa an dakatar gaba ɗaya, kuma a lokacin ta yi finafinai da yawa duk ba su fito ba ne ba, sannan sun ci gaba da fitowa ɗaya bayan ɗaya sai ya ke ganin cewa kamar ba a daina ba. Sai ya ɗauke ni ya kai ni ƙara wurin ‘yan Hisbah ko in ce a lokacin ba ma ni ya kai ba yarinyar ya fara kaiwa. To daga nan sai yayan nawa ya kai ni Hisbah, aka rufe ni. Don gaskiya a Hisban nan na sha wahala don har aski su ka yi mani, su ka dake ni sosai. Daga ƙarshe shi yayan nawa ya ga dai ban yi laushi ba, sai ya ɗauki kes ɗin nawa ya kai shi NAPTIP kamar ‘human right (abuse)’ haka dai. Can ma dai su ka kulle ni, don aƙalla na kai kamar sati uku a kulle!
“A lokacin, ita ma yarinyar ta na hannun su kuma sun kirawo Adamu ya zo da Umar Kanu da su Fati Muhammad. Amma duk ba wai sun zo ba ne saboda an kirawo su a kan a taɓa mutuncin su ko waye, kawai dai ana so a tambaye su wasu bayanai game da yarinyar.
“Lokacin dai sati na uku, ita kuma yarinyar ta yi wata a gurin su. Ba zan taɓa mantawa ba da su ka kirawo Adamu ya zo su NAPTIP ɗin, su ke ƙoƙarin nunawa yarinyar ai ba ta da wani gata ko waye su ke so lallai sai sun damƙa yarinyar a hannun Adamu ta ci gaba da zama.
Aka kirawo Mama na, aka kirawo Adamu. Lokacin ni ba ma na gurin, don ban yi aure ba, aka tambayi yarinyar, ‘Ke, gun wa za ki zauna?’ Yarinya ta ce ita za ta zauna a gurin Yasir saboda Yasir tare aka san mu da ita tun ta na ƙarama.
“Ni na yi ɗawainiya da yarinyar nan; na kai ta makarantar boko, na kai ta Islamiyya; duk wani irin kamar rashin lafiya, na kai ta asibiti, duk ni ne dai, tun kan ta zo ta fara fim har ta zo ta fara, har ma iyanzu.”

Ya ce abin da ya ke so ya fahimtar da mutane shi ne su san cewa Adam A. Zango ba shi da alaƙa da Ummi Rahab ko ta kusa ko ta nesa.
Ya ce, “Bayan hukuma sun ba mu dokoki, a lokacin yarinyar ta ɓace a industiri, ni ma na ɓace. To gaskiya a wannan shekarun – shekara bakwai – gaskiya ban san wani abu da Adamu ya tura wa yarinyar nan ko kuma ni ya tura min ya ce na ba ta ba. Bai san ɗawainiyar ta ba, bai san cin ta ba bai san shan ta ba, bai san suturar ta ba; ko rashin lafiya bai san muhimman abubuwa na cikin rayuwar ta ba. To a wannan shekarun irin an shiga shekara na takwas Adamu ya kirawo ni a waya ya ce min don Allah yarinyar nan ya na so zai yi wani aiki da ita, fim ɗin ya cancanci Ummi. To a lokacin Ummi ba ta kai ‘under-age’ ba, gaskiya. Sai na ce, gaskiya ka yi haƙuri don ni a lokacin ma ba na iya faɗin sunan shi saboda ina ganin mutuncin sa; ko na ce masa Prince ko na ce masa Yallaɓai. Abin da na ke ga ya masa kenan.
“A lokacin sai na ce ka yi haƙuri na san Ummi yau ba abin da zan iya yi a kan wannan abin saboda ba ta kai lokacin da za ta fara fim ba ko in ta kai lokacin ko na bar ta ko kar na bar ta ko ba na raye, ko ta yi sha’awa za ta iya yi. Na ba shi haƙuri dai; a lokacin ya ce min to ba matsala.
“Bayan kuma an ƙara shekara ɗaya ne sai Adamu ya kirawo ni a kan maganar Ummi, a kan in Ummi ba ta da manema shi ya na so zai aure ta, don lokacin ba zan manta ba, ina Katsina. MZu ka yi magana da shi ta fahimta da ya yi maganar auren nan.
“A lokacin na san da man yarinyar ba za ta ƙi ba don ta na ƙaunar sa ba laifi.
“Sai na kirawo Umar Kanu na ce masa, ‘Ka ji ka ji, ga abin da Adamu ya ce min.’ Sai ya ce in da gaske ne ai da man haka ya fi tunda aure shi ne mutuncin ‘ya mace.
Sai na ce masa ni ma dai abin da na ke so kenan; na fi son Ummi ta yi aure a kan fim ɗin nan wallahi. Sai ya ce min ba matsala, ka tabbatar da hakan.
“Mu ka ƙara magana da Adamu dai ta waya dai a kai a kai a kan maganar auren yarinyar, har na samu har na zo gida ma na ke cewa, ‘Ummi, kin ji kin ji’.
“Ta ce min, ‘Wallahi Yaya ba matsala. Ai ni na san ba za ka yi abin da zai cuce ni ba.”
“Sai na ce, ‘A’a, yadda na ke ƙaunar ki haka shi ma ya ke ƙaunar ki.’
“Ya ce mani idan zai auri yarinyar nan bai buƙatar a yi fati ko a yi wani dina. Na ce, ‘Ai wannan duk ba shi ne aure ba, kawai dai aure ya na buƙatar a sa manya, a bada sadaki, a yi aure.’ Sai ya ke ce min ba matsala. Ya ce min maman sa za ta zo Kano, in ta zo Kano Ummi za ta je su gaisa, su yi wasu maganganu.
“A lokacin ma ban san me su ka ce ba. Ina dai Katsina, sai Ummi na kirawo maman mu; a waya lokacin ma ba waya a wurin Ummi, na kirawo maman mu a waya na ce ta ba ni ita. Na gaya mata, ‘Kin ji kin ji kin je can wajen mahaifiyar Adamu, amma kar ki je ke kaɗai, ki ɗauki Hafsa yayar ki, sai ku je tare. To sai ta ɗauki Hafsa su ka tafi, bayan sun je ban san dai me su ka tattauna ba.
“Bayan sun dawo, mun ƙara waya da shi. Sai ya ke ce min ai ta je sun tattauna amma don Allah ya na buƙatar a yi abIn nan, a sa rana. Na ce mai, “Ba matsala, ai komai abin ya na gun ka, don haka ina muku fatan alheri.
“Ni dai a lokacin, Adamu mun gama magana da shi a kan cewar zai turo manyan sa don har manya na ma na gaya wa ni kai na, wanda su ke a matsayin iyaye a wajen mu daga ni har yarinyar. Don a lokacin ni ba zan iya karɓar manyan sa ba sai na gaya wa mahaifi na da mahaifiya ta, su ka ce ba matsala Allah ya kawo su.
“Maganar mu ta ƙarshe kenan a kan zai turo manyan sa.
“Mun sa lokaci da shi kuma lokacin ya zo Adamu bai kira ni ba, kuma bai turo manyan sa ba. Da dai har zan kirawo shi, amma ban kirawo shi ba dai gaskiya.
“Sai da aka kai sati ɗaya sati biyu sai na ɗauki waya na kirawo Adamu. Na yi masa kira biyu bai ɗaga ba, sai na rabu da shi, ban ƙara ce masa komai ba.
“To ni dai bai ce min yarinyar nan ya fasa auren ta ba, bai kuma ce min za a yi auren ba. Ban ƙara jin sa ba kwata-kwata!

“Mun rabu da shi dai ba mu ƙara sa shi a idon mu ba, daga ni har yarinyar.
“To bayan kamar shekara ɗaya dai sai Adamu ya ƙara kira na a waya, don ba zan taɓa mantawa ba, yarinyar ta tafi biki ita da ‘yan’uwa, ya kirawo ni zai wani aiki (mai suna) ‘Farin Wata’ da sauran su, waye waye, Idan Ummi ta na buƙata. Bayan ni kuma waccan maganar da mu ka yi, sai ni a tunani na ina ganin misali, in sun yi aikin za su yi auren ko yaya ne, ni ban sani ba dai.
“Kawai dai ya kira ta labarin ‘Farin Wata’. Kawai sai na karɓa na ce masa ba matsala tunda da man Ummi ta na min maganar ma ta na so ta koma industiri kuma na mata alƙawari zan mata jagora tunda ba wani wanda zai mata alƙawari, in ba ni ba ba wanda zai mata jagora sai kuma Allah, ba ni ba, Allah ne zai mata jagora.”
Ya ce, “Don haka Ummi sun je sun yi aikin ‘Farin Wata’, don kafin ma su yi sai da mu ka karɓi fom na kamfanin sa, mu ka je nan Hukumar Tace Finafinai ta Kano, ni na sa mata hannu mu ka je can Censor na can NTA ma, can ma aka kawo wani na sanya hannu. Komai ni na yi sa hannu a kan aikin Ummi wanda ta yi na ‘Farin Wata’, ta je ta yi aikin ‘Farin Wata’. Aka ɗauke ta. Satin ta biyu a can ana aikin. Bayan ta gama aikin, ta bugo min waya ta na hanya za ta dawo; bayan sati biyu kenan.
“Da ta dawo, ta dawo da kuɗin ta kuɗin aiki N35,000. Ta zo min da su gida ta ce min wai ga su nan, ‘Ga abin da na samo na aiki na, N15,000 na aikin ‘Farin Wata’,’ wanda Adamu ya ba ta. Ta ce min kuma N20,000 ga shi akwai wani ko yaron sa ne, wani Sammani, wanda kwanaki ma hotunan su su ka yi ta yawo da yarinyar ana cewa wai ta yi aure ta yi aure, kuma da man ba aure ba ne, hoto ne kuma fosta ce ta woƙoƙin da su ka yi.
“To, wannan kuɗin waƙar ne, kuɗin ya biyo ta hannun Adamu, Adamu ya karɓi N20,000 na wannan waƙar da za a yi, su ne kuɗi 35,000. Don a lokacin ma ta ɗauki kuɗin ta je kasuwar Ibo Road ta sayo kayayyaki wanda za su yi waƙar tare, don ko ƙwandala ma a kuɗin yarinyar ma ba ta taɓa a kuɗin ba.”
Bugu da ƙari, Yasir ya kuma yi cikakken bayani kan batun da ake ta yi na Ummi Rahab ta butulce wa Adam A. Zango, ya ce: “Ni dai abin da na ke so na nuna wa mutane shi ne da ake ta kalma guda ɗaya a kan yarinyar nan, ta yi butulci, butulci, butulci, to ni dai a iya tunani na ban ga wani abin butulci a nan ba.
“Ana ta maganar butulci, to ni wannan abin ya taɓa ni sosai, ya taɓa min zuciya ta saboda ni a iya tunani na a cikin shekara goma sha ukun nan da yarinyar nan ta ke rayuwa tare da ni da ita bai san cin ta ba bai san shan ta ba, bai san suturar ta ba, bai san rashin lafiyar ta ba, bai san komai nata ba. Don Allah jama’a, tsakanin shi da yarinyar nan waye ya yi wa wani butulci?
“Saboda ni a iya tunani na, wallahi ban taɓa tunanin zan fito ni na yi magana ba. Saboda me? Saboda ni har yanzu mutumin nan har yanzu a zuciya ta da sauran mutuncin sa, ita kan ta yarinyar ita ma haka.
“Ni abin da ya sa na fito na yi magana shi ne na ji mutane kala-kala su na ta cewa yarinyar nan wai butulu ce, butulu ce! Abubuwan sun taɓa ni sosai yadda ba kwa tunani.
“Don Allah abin da na ke so mutane ku fahimta a iya wannan labarin da na bada, tsakanin Adamu da yarinyar nan waye ya yi wa wani butulci? Shin Adamu ne ya yi wa Ummi butulci ko kuma Ummi ce ta yi wa Adamu butulci?
“Kuma da ta ke maganar za ta tona asiri a kan wannan maganar, aure ne ya ce zai aure ta kuma Allah dai bai yi ba, sannan kuma ba ya so ta kula kowa. Wannan maganar da ya ke cewa wai ai shi in ya ce wa mutum a matsayin sa don ya na matsayin kamfanin sa in ya ce ya yi nan shi ba ya so ya ga ya na yin wani guri, to duk mutumin da a rayuwa ka na kyautata masa ba zai guje ka ba a iya tunani na ma kenan, duk ko ma waye, tunda ni a iya tsawon shekaru na da yarinyar nan da a ce na zalunce ta ko ina mata wani abu wanda zai ɓata mata rai a ‘yan shekarun nan, da tuni ta guje ni tunda ba ni na haife ta ba. In da ban baI wa yarinyar nan tarbiyya ba, da ta ya za ka fito ka ce za ka aure ta?
“Kuma yarinyar nan a lokacin da ka ce za ka aure ta ta na da manema da yawa, to amma saboda darajar ka mun ce ta dakata don mun ce ta dakatar da kowa a lokacin.
“Saboda haka, ni ina ganin cewa yarinyar nan ta na da tarbiyya daidai wacce mu ka ba ta. Sannan kuma da ka ke ta maganar yawo-yawo, mu Ummi ba mu san ina ta ke zuwa yawo ba, don kullum ta na gida. Hasali ma, sau da dama za ka kira ni ka ce in haɗa ka da ita, in ɗauki waya in ba ta. Wani lokacin in ka kira ni ba na gida zan ce maka ba na gida, idan na dawo zan ba ta. Kuma wani lokacin ma sau nawa zan dawo na kira ka, sau nawa ba za ka ɗauka ba kuma ba za ka biyo baya ba?”

Yasir ya ƙara da cewa: “Abin da ya fi taɓa min zuciya, ya ƙona min rai sosai fiye ma da kowane abu, da ake maganar Ummi ba ta da asali. Ba ta da asali? Ummi ta na da asali, domin Adamu kai ka je ka ga iyayen yarinyar. Da za ka tafi Saudiyya na ɗauki lambar wayar mahaifiyar ta na ba ka ka gan ta. Da kai da Afakallahu da Rarara kun je kun gaisa da ita, a lokacin ma har magana ka yi mata.
“To saboda haka Ummi ta na da iyaye; da mahaifin ta da mahaifiyar ta. Bayan lokacin da ka dawo daga Saudiyyar ma ka zo ‘family’ ɗin mu kai da Tahir Fagge da Abu Sarki gaida ƙanwar maman mu har gida.”
Ya nemi jama’a da su yi masu adalci kan wannan batu tsakanin Zango da Rahab.
Yadir M. Ahmad ya ƙarƙare da cewa a duk maganganun da ya faɗa akwai wadda ba daidai ba, to Allah ya saka wa Zango, sannan kuma idan akwai abin da ya faɗa na ƙarya, to jarumin ya fito ya ƙaryata shi.
Comment: gasky Allah ya kyauta kawai