• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ministan Yaɗa Labarai ya yi alƙawarin tallafa wa gidan Rediyon EFCC

by WAKILIN MU
May 17, 2024
in Nijeriya
0
Ministan Yaɗa Labarai ya yi alƙawarin tallafa wa gidan Rediyon EFCC

Alhaji Mohammed Idris yana jawabi a wajen ƙaddamar da EFCC Radio

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi alƙawarin tallafa wa manufofin gidan rediyon Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai suna EFCC Radio.

Idris ya bayyana hakan ne a wurin taron ƙaddamar da gidan rediyon da ke kan lamba 97.3 a zangon FM wanda aka yi a hedikwatar hukumar a Jabi, Abuja a ranar Alhamis, 16 ga Mayu, 2024.

Ministan ya ce: “Ku tabbatar da cewa a matsayi na na Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, zan yi duk abin da zan iya don tallafa wa manufofin ku.”

Kafin yin wannan iƙirarin, ministan ya bayyana jin daɗin sa “da halartar wannan bikin ƙaddamar da sabuwar hanyar sadarwa a Nijeriya, wato EFCC Radio 97.3 FM.

“Dole ne in ce abin farin ciki ne sosai ganin ɗaya daga cikin manyan hukumomin tabbatar da doka da oda a ƙasar nan na ƙara faɗaɗa hanyoyin sadarwar jama’a da gudanar da ayyukan su ta hanyar kafa gidan rediyon FM.

“A matsayin ta na hukumar da ke fuskantar jama’a, haƙiƙa yana da matuƙar muhimmanci Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC) ta tsara labaran da ke tattare da duk wani muhimmin yaƙi da ake yi da cin hanci da rashawa a ƙasar mu a tsanake da dabaru.”

Ana tattaunawa da Alhaji Mohammed Idris a sabon gidan Rediyon EFCC

Ya kuma yi alƙawarin cewa, “Tare da yin aiki ta hannun Hukumar Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC), za mu kuma tabbatar da cewa mun ƙarfafa gwiwar sauran hukumomin gwamnati da abin ya shafa su yi haka, tare da bayar da gudunmawa wajen faɗakarwa da wayar da kan jama’a.”

A cewar ministan, “Ajandar mu ta biyu cikin 5 a Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ita ce inganta manufofi da tsare-tsare na Gwamnatin Tarayya, kuma ina farin ciki da cewa a yanzu mun samu wannan sabuwar abokiyar hulɗa, EFCC Radio 97.3. FM, wacce za ta taimaka mana wajen cimma wannan manufa.

“Abu na farko na waccan ajandar mai ƙunshe da abubuwa biyar shi ne dawo da amana a harkokin sadarwar jama’a a Nijeriya.

“Ina so a kan haka, in umarci masu gudanarwa da ma’aikatan wannan sabuwar tashar, da su yi ƙoƙari su yi aiki a kowane lokaci bisa ƙa’idoji na aikin watsa labarai da aikin jarida.

“Ku ne abokan hulɗar mu masu ƙima yayin da muke neman sake ginawa da dawo da yardar al’ummar Nijeriya kan bayanan da ke fitowa daga Gwamnatin Tarayya.

“A kan haka, bari in sake taya Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC) murna, kan wannan rawar da ta taka. Ina yi maku fatan alheri yayin da kuka fara aiki gaba ɗaya.”

Loading

Tags: EFCC RadioMohammed Idris
Previous Post

Gwamnan Kano ya ba da naira miliyan biyar kan rashin lafiyar jarumar Kannywood Halisa Muhammad

Next Post

MOPPAN ta taya Afakallahu murnar naɗin da Shugaba Tinubu ya yi masa

Related Posts

Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Next Post
MOPPAN ta taya Afakallahu murnar naɗin da Shugaba Tinubu ya yi masa

MOPPAN ta taya Afakallahu murnar naɗin da Shugaba Tinubu ya yi masa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!