GWAMNAN Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ba da gudunmawar N500,000 ga tsohuwar jarumar Kannywood, Hajiya Halisa Muhammad, kan rashin lafiyar ta.
Mai ba gwamnan shawara kan harkokin jinƙai, Malama Fauziyya D. Sulaiman, ta bayyana hakan a soshiyal midiya a ranar Talata.
Ta ce, “Alhamdu lillah. Mai girma Gwamnan Kano, H.E Abba Kabir Yusuf, ya biya wa Halisa Muhammad (‘yar fim) kuɗin aiki naira miliyan biyar (5ml). Allah ya saka wa mai girma gwamna da alkhairi, amin ya Allah.”
Idan ba ku manta ba, a kwanan baya Halisa ta saki wani bidiyo inda a ciki ta nemi gudunmawa a wurin al’umma, ta ce ta na neman zunzurutun kuɗi har N6,030,000 na wata allura da za a riƙa yi mata har sau 18, kuma duk ɗaya N335,000 take.
A lokacin da ta nemi taimakon, abokan sana’ar ta ‘yan fim sun tara mata sama da N3,000,000.

Tun a wancan lokacin bayan ɓullar bidiyon neman taimakon, da dama sun tofa albarkacin bakin su a kan cewa wanda su ka samu dama a cikin gwamnatin Kano irin su Abba El-Mustapha, Sanusi Oscar 442 da Fauziyya D. Sulaiman su taimaka su yi wa gwamna magana ko za a dace.
Cikin hukuncin Allah ga shi an dace gwamnan ya taimaka.