SHUGABAN Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Dakta Ahmad Muhammad Sarari, ya taya jarumi Abba El-Mustapha murnar naɗin da gwamnatin Jihar Kano ta yi masa a matsayin sabon Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano (KSCB).
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na MOPPAN, Malam Al-Amin Ciroma, ya fitar a yau, wadda mujallar Fim ta samu kwafe ɗin ta, an ce, “Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Muhammad Sarari, a madadin ƙungiyar MOPPAN, ya na taya Abba El-Mustapha murnar naɗin da Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi masa a matsayin sabon Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano (KSCB).
“MOPPAN ta yi matuƙar farin ciki da jin labarin cewa gwamnan jihar Kano ya naɗa ɗaya daga cikin ‘ya’yan masana’antar Kannywood matsayin shugaban hukumar da ake da kima.
“Ya lura da cewa El-Mustapha ya cancanci wannan naɗi tare da addu’ar Allah ya ba shi nasarar gudanar da aikin sa, kana kuma ya ƙara wa Kannywood bajinta.”

Ita ma ƙungiyar dattawan Kannywood ta ‘Kannywood Foundation’ ta taya El-Mustapha murnar samun wannan matsayin.
A cikin saƙon taya murnar wanda daraktan hulɗa da jama’a na ƙungiyar, Alhaji Muhammad Kabiru Maikaba, ya fitar a yau, ƙungiyar ta ce, “Bisa sahalewar majalisar ƙoli ta wannan cibiya mai albarka, mu na taya Abba El-Mustapha murnar zaɓen sa da zaɓaɓɓen Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya yi a matsayin shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano (KSCB). Gaba ɗayan mu shugabanni da ‘ya’yan wannan cibiya na matuƙar farin cikin samun tabbacin wannan muhimmin labari.
“Don haka mu ke yi wa Allah mai girma godiya, sannan mu na son mu nuna wa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, dangane da irin wannan karamci da ƙauna da ya nuna wa wannan masana’anta. Mu na taya shi addu’a Allah ya taya shi bisa duk wata niyya ta alheri da ya bijiro da ita don ciyar da jihar gaba.
“Haƙiƙa, ɗora Abba na Abba a kan wannan kujera ya kasance an ɗauki ƙwarya an ɗora a kan gurbin ta.
“Jajircewa da kwarjini, wannan ya tabbatar mana da wani haske da ya nuna mana hanyar ci-gaba ɗoɗar a wannan masana’anta.
“Allah ya yi ma jagora, kuma ya albarkaci duk abin da ka sa a gaba. Allah ya kare ka daga sharrin maƙiya da mahassada, mutum ko aljani.”