ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya, MOPPAN, reshen Jihar Kebbi ta zaɓi sababbin shugabanni.
Ƙungiyar ta gudanar da zaɓen ne a ranar Asabar, 19 ga Oktoba, 2024, da misalin ƙarfe 11:00 na safe, a makarantar firamare da sakandare na Ƙauran Gwandu da ke cikin garin birnin Kebbi.

Kamar yadda sabon Sakataren Ƙungiyar, Malam Nasir Umar Gwandu ya shaidawa mujallar Fim, ya ce, “Zaɓen ya samu sa idon Babban Darakta na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Al’adu ta Jihar Kebbi, Alhaji Shehu Galadima Zila (Ɗan Galadiman Kola).”

Haka kuma, Alhaji Abubakar Tafida, babban ma’aikacin gwamnati daga ‘Local Government Service Commission’, shi ne wanda ya jagoranci kwamitin zaɓen.
An gudanar da zaɓen lami lafiya, babu hamayya ko kuma tashin hankali, tunda a kan yarjejeniya (consensus) zaɓen ya gudana.
Bayan zaɓe ya kammala, sai Barista Abdulrazaq Muhammad ya rantsar da sababbin shugabannin, inda nan take su ka kama aiki.

Jihar Kebbi ta na ɗaya daga cikin jihohi da uwar ƙungiyar ta ƙasa ta ba umarnin gudanar da zaɓe kafin zuwan na ƙasa baki ɗaya, wanda zai gudana a Janairun 2025.
Kuma an ba su wa’adi zuwa ƙarshen watan Nuwamba, duk jihar da bata gudanar da zaɓe ba, wakilan ta ba za su yi zaɓen uwar ƙungiya ta ƙasa ba.
Sauran jihohin sun haɗa da Gombe, Kogi, Kwara, Katsina da Zamfara.
Jerin sunayen sababbin shugabannin:
1. Chairman: Bashir Inuwa Isah
2. Vice Chairman: Hajiya Habiba Ɗanjumma Manga
3. Secretary: Nasir Umar Gwandu
4. Asst. Secretary: Ibrahim Umar
5. Treasurer: Ibrahim S/Fulani
6. Financial Secretary: Al-Amin Suleiman
7. P. R. O (1): Ahmad Aliyu Kukah
8. P. R. O (2): Mahrazu Umar Maurida
9. Organizing Secretary: Faruk G. Nato
10. Asst Organizing Secretary: Shamsu Attahiru Utono
11. Auditor: Lawal Abubakar Mahuta
12. Welfare Officer (1): Suwaiba Abubakar Atiku
13. Welfare Officer (2): Hauwa’u A. S. Marafa
14. Displinary Officer (1): Sheriff Ibrahim Babangida
15. Displinary Officer (2): Sadiq Tarasa
16. Displinary Officer (3): Mustapha Ahmed Kukah
17. Displinary Officer (4): Fatima Mohammed Kangiwa