• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 25, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

MOPPAN ta fitar da ƙa’idojin tsayawa takara

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
September 28, 2021
in Labarai
0
MOPPAN ta fitar da ƙa’idojin tsayawa takara
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HAƊAƊƊIYAR ƙungiyar masu shirya finafinai ta Kannywood (MOPPAN) ta ƙaddamar da sayar da takardar neman shugabancin ƙungiyar a matakai daban-daban.

Shugaban kwamitin shirya zaɓen, Malam Ahmad Salihu Alkanawy, da sakataren kwamitin, Dakta Ahmad Salihu Bello, sun faɗa a wata takarda da su ka rattaba wa hannu cewa duk mai neman zama Shugaban ƙungiyar dole sai ya cika sharuɗɗa kamar haka:

1. Ya zamana ya na da ƙwarewa a cikin industiri ta tsawon shekara goma.

2. Ya zamana ya samu shaidar kirki.

3. Ya zamana ba shi da wata shaida ta almubazzaranci a sha’anin kuɗi.

4. Ya zamana ba shi da wata tuhuma da ta shafi cin ta’addanci.

5. Ya zamana ya na da duk wata nagarta ta shugabanci a matakin ƙasa.

6. Sai ya biya kuɗin takardar tsayawa takara.

Wanda zai tsaya takarar Mataimakin Shugaba na 1 zuwa na 3 dole ya bi ƙa’idojin da aka gindaya wa ɗan takarar zama Shugaba.

Shi ma mai neman kujerar Sakatare dole ya cika irin ƙa’dojin da mai neman Shugaba ya cika.

Mai neman kujerar Ma’aji kuwa, dole ya cika ƙa’idoji kamar haka:

1. Ya zamana ya na da ƙwarewa a cikin industiri ta tsawon shekara biyar.

2. Ya zamana ya samu shaidar kirki. 

3. Ya zamana bai da wata shaida ta almubazzaranci a sha’anin kuɗi.

4. Ya zamana ba shi da wata tuhuma da ta shafi ta’addanci.

5. Ya zamana ya na da duk wata nagarta ta zama Ma’aji a matakin ƙasa.

6. Dole ya biya kuɗin takardar tsayawa takara.

Ƙa’idojin sauran kujerun su ne:

1. Ɗan takara ya zamana ya na da ƙwarewa a cikin industiri ta tsawon shekara biyar.

2. Ya zamana ya samu shaidar kirki.

3. Ya zamana ba shi da wata shaida ta almubazzaranci a sha’anin kuɗi.

4. Ya zamana ba shi da wata tuhuma da ta shafi ta’addanci.

5. Ya zamana ya na da duk wata nagarta a kujerar da ya nema.

6. Dole ya biya kuɗin takardar tsayawa takara.

Shugabannin kwamitin sun kuma bayyana cewa dole ne duk mai neman shugabancin wannan ƙungiya da mataimakan sa su fito daga shiyyoyin ƙasar nan uku kamar haka:

1. Mataimakin Shugaba na 1 – Arewa-maso-gabas.

2. Mataimakin Shugaba na 2 – Arewa ta Tsakiya.

3. Mataimakin Shugaba na 3 – Arewa-maso-yamma.

Haka kuma ana so masu neman waɗannan muƙamai su ɗauki hotunan takardar izinin shiga zaɓen su tura wa wannan imel: sardaunanfce@gmail.com.

Bugu da ƙari, sanarwar ta ce dukkan ‘yan takara za su hallara a gaban kwamitin zaɓe domin a tantance su a ranar jajibirin zaɓen.

Fom ɗin shiga takarar MOPPAN ta bana

Haka kuma dole ne ‘yan takarar su zo da ainihin takardar shiga takarar da kuma shaidar biyan kuɗi ta banki domin tabbatarwa.

Sannan dole kowa ya gabatar da katin shaidar sa.

A ƙarshe, dukkan wanda aka wakilta dole ne ya zo da shaidar kati.

Bugu da ƙari, an bayyana farashin fom-fom na tsayawa takarar kowane muƙami kamar haka:

i. Shugaba – N50,000

ii. Mataimakin Shugaba na 1 zuwa na 3 – N40,000

iii. Sakatare – N40,000

iv. Ma’aji – N30,000

v. Sakataren Kuɗi – N30,000

vi. Mataimakin Sakatare – N30,000

vii. Kakaki – N30,000

viii. Mai Binciken Kuɗi N30,000

ix. Mai Binciken Kuɗi – N30,000

x. Mataimakin Sakatare – N30,000

xi. Mai Kula da Walwala (mace kawai) – N30,000

An bayyana cewa duk wanda zai sayi fom, to ya tura kuɗin zuwa asusun banki kamar haka:

Mohammed Ibrahim Gumel, Access Bank, No.  0040001335.

Loading

Tags: Ahmad AlkanawyDakta Ahmad S. Bellohausa filmsKannywoodMOPPANzaben MOPPAN
Previous Post

Abdullahi Ubangari ya zama angon Zulaihat

Next Post

‘Yartsana: Ninƙaya cikin kogin karuwanci

Related Posts

Labarai

Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar

July 24, 2025
‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Next Post
Littafin 'Yartsana da marubuci Ibrahim Sheme

'Yartsana: Ninƙaya cikin kogin karuwanci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!