HAƊAƊƊIYAR Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kano, ta yi kira ga jama’a da su taimaka wa wasu ‘yan fim waɗanda su ka haɗu da iftila’i na ƙona masu shaguna da ofisoshi da kayyakin su da wasu ɓata-gari su ka yi a Kano bayan an faɗi sakamakon zaɓen gwamnan jihar.
Mujallar Fim ta ruwaito yadda ɓata-garin su ka kai hari ofisoshin ‘yan fim irin su Dauda Kahutu Rarara da Rabi’u The King, su ka farfasa kayayyaki tare da ƙona ofisoshin saboda bambancin ra’ayin siyasa a ranar da aka bayyana cewa ɗan takarar zama gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, shi ne ya lashe zaɓen.
Jagororin MOPPAN sun kai ziyara wuraren da abin ya faru kafin su yanke shawara kan yadda za a yi a taimaki waɗanda abin ya shafa, inda daga nan su ka fara tara kuɗin gudunmawa.
A cikin wani saƙon murya da ya yaɗa a guruf-guruf na WhatsApp, kakakin ƙungiyar MOPPAN reshen Kano ɗin, Malam Misbahu M. Ahmad, ya faɗi irin ƙoƙarin da su ka yi wajen kafa gidauniyar tallafin. Ya ce, “Assalamu alaikum wa rahatullahi wa barakatuhu. ‘Yan’uwa ina yi maku addu’a irin ta addinin Musulunci, da fatan mun sha ruwa lafiya. Ubangiji Allah ya karɓi ibadun mu.
“Kamar yadda aka sani cewa abubuwa sun faru, wanda za a ce iftila’i ne ga ‘yan’uwan mu, abokan sana’ar mu, bayan sakamakon zaɓe a nan Jihar Kano, waɗanda su ka samu jarabawa na ƙone-ƙonen kayayyakin da aka yi da sace-sace na kwashe-kwashe da farfasa masu wasu abubuwa, wanda wannan abubuwa sun shafi kayayyaki kacokam, wanda wannan masana’anta ta ke alfahari da su na kasuwanci.
“Wannan ya sa wasu ƙungiyoyi, musamman mu MOPPAN reshen Jihar Kano, mu ka yi tattaki mu ka je mu ka dudduba waɗannan abubuwa, mu ka taya su alhini, mu ka yi jaje.
“To, duba da yadda mu ka ga abubuwan da irin asarar da aka tafka da halin da su ke ciki, ‘yan’uwan mu ne, mu ka dawo gida mu ka zauna, mu ka yi ta nazari, mu ka yi ta tunani, duk da dai mun ɗan yi bayani a gidaje irin waɗannan, na cewa waɗanda ba su je ba, su je, waɗanda kuma su ka je, ya kamata su kalli abin nan a tausaya, mu ga hanyar da za a bi mu yi wani tallafi wanda tallafin nan zai ɗan rage raɗaɗi ko duba halin da ake ciki na halin azumi, mutum magidanci ya wayi gari wurin sana’ar sa a ƙone ko a rushe, babu inda zai je ya fito ya samu ko abin kunu da zai kai wa iyalan sa. In ma ya na da shi, yanzu dai ya tsaya.
“Wannan ya sa mu ka yi kiran mitin na gaggawa, mu nan MOPPAN reshen Jihar Kano, mu ka zauna mu ka fitar da shawarwari, wanda daga cikin shawarwarin ita kan ta ƙungiyar Allah ya sa ta na da ɗan wani abu a jakar ta a ajiye, aka ɗauko aka ce to a ba waɗannan ‘yan’uwa gudunmawa ta N100,000, wanda ita ƙungiyar ce reshen Jihar Kano ta bayar, su tsinka su samu wanda za su sayi sikari.
“Duk da haka, su kan su exco ɗin su ka ce ya kamata kowa a jikin sa ya ciro wani abu. Don haka mu ka yi ‘taxing’ ɗin kan mu kowa ya ba da N10,000, aka ce a saka dai a ciki. Jimillar kuɗi kusan N220,000 in-sha Allahu.
“Duba da wannan, mu ka ce za mu yi amfani da wannan dama mu kira ‘yan’uwa na sauran ƙungiyoyi da ‘elders’ da shugabanni, da ɗaiɗaikun mu masu hannu da shuni waɗanda ya kamata su tallafa, mu taimaka wa mutanen nan don girman Allah.”
A madadin ƙungiyar, Misbahu ya yi kira ga ‘yan fim da su watsar da bambance-bambancen da ke tsakanin su, su agaza wa waɗanda abin ya shafa.
Ya ce: “Don Allah kada ka kalli mutum a matsayin wai ba naka ba ne ko ba ya yin ka ko ba jam’iyya ta haɗa ku ba ko wani abu na siyasa. Mu kalli masana’antar, mu kalle su a matsayin ‘yan’uwa, wanda da ma ‘yan’uwan ne.
“Yau in kun duba, idan don siyasa aka yi, babu wani ɗan siyasa da ya fito ya tallafa masu ko ya ke jaje, an bar mu da halin mu da ‘yan’uwan mu ne. Kun ga kenan dole mu yarda cewa mu ‘yan’uwa ne Allah ya haɗa mu a cibiya ɗaya mu na cin abinci, yanzu ga iftila’i ya zo an bar mu mu ke jajanta wa ‘yan’uwan mu.
“Don Allah, don girman Allah, don wannan wata da mu ke cikin alfarmar sa, masu neman lada ga fa abin da ya kamata mu yi, ‘yan’uwan mu su na cikin wani hali, a zaune su ke a shagunan su, wajen nan a ƙone, sai damuwa, sai tunanin dukiyoyin mutane da wanda ya ke nasu ne da wanda ya ke na hannun mutane ne, na ajiya ne wani aka ba ka, wani na aiki ne aka ba ka ba ka gama ba, wani ka gama ba ka kai ba asara ta biyo baya. Ba duka mutane ne za su ɗauki asara ba su ce sun haƙura, wani sai an yi ƙiƙi-ƙaƙa, an kai ruwa rana. Don Allah, don girman Allah mu taimaka wa mutanen nan.
“Don haka ga ƙofa nan a buɗe, ga ‘account number’ nan, mu na so nan da kwana biyar zuwa goma, abin da aka tattara a ba mutanen, saboda su samu dama da za su je su yi walwala ko ƙaƙa ne mu daina ganin su cikin ɓacin ran nan. An san ba za a mayar masu kwatan abin da su ka yi asara ba, amma dai ‘yan’uwa ne mu taimaka. Mu ma mun taimaki kan mu, na waje ma zai ji daɗin taimakon mu.
“Kuma duk da haka za mu ci gaba da bin sauran ƙungiyoyi ko da ba na Kannywood ba ne, da sunan wannan ƙungiya ta MOPPAN reshen Jihar Kano, mu nema masu tallafi na taimako. Don Allah, don Annabi mu taimaka masu, don Allah, don girman Allah. Wassalamu alaikum wa rahamatullah.”
Wasu daga cikin waɗanda su ka fara ba da wannan gudunmawa dai su ne:
1. MOPPAN reshen Jihar Kano, N100,000
2. Ado Ahmad Gidan Dabino (MON), N10,000
3. Sunusi Garba Kalambaina, 10,000
4. Misbahu M. Ahmad, N10,000
5. Asma’u Sani, N10,000
6. Hayatu Yakubu, N10,000
7. Sulaiman Abubakar, N10,000
8. Sudais Ahmad, N10,000
9. Mubarak Abba, N10,000
10. Kamal S Alƙali, N10,000
11. Nura Sharu, N10,000
12. Isma’il Khalil Ja’en, N10,000
13. Galadima Muhammad, N10,000
Jimillar abin da aka tara shi ne N220,000.
Misbahu ya ba da bayanin asusun da za a saka gudunmawar kamar haka: Sulaiman Abubakar Yahaya, Jaiz Bank, lamba 0000030353.