• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Alƙali ya mayar da shari’ar jarumar Kannywood Hadiza Gabon zuwa kotun Musulunci

by DAGA ALI KANO
March 3, 2023
in Labarai
0
Hadiza Aliyu Gabon

Hadiza Aliyu Gabon

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WATA Kotun Majistare da ke Magajin Gari, Kaduna, a yau Juma’a ta mayar da shari’ar nan da ake gwabzawa tsakanin jarumar Kannywood Hadiza Aliyu Gabon da wani mutum zuwa Babbar Kotun Shari’ar Musulunci.

Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin yadda wani ma’aikacin gwamnati mai suna Bala Musa ya yi ƙarar Hadiza a kan zargin wai ta yi masa zamba cikin aminci, ta ci kuɗin sa amma ta ƙi auren sa.

An yi zaman kotun har kusan sau huɗu ana ɗagawa, amma da aka koma kotu a yau sai alƙalin, Malam Isiyaku Abdulrahman, ya bayyana mayar da shari’ar zuwa Babbar Kotun Musulunci da ke Tudun Wada.

Hakan ya biyo bayan ƙorafin da lauyan mai ƙarar, Barista Nurudeen Murtala, ya yi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa a yayin da ya ke bayyana mayar da shari’ar zuwa wata kotun, alƙalin ya zargi lauyan da ƙoƙarin ɓata wa kotun lokaci.

Ya ce: ”Ka na da zaɓi biyu. Na ɗaya ko dai in yi watsi da ƙarar ko in mayar da ita ga wata kotun.”

Shi dai Bala Musa, ya kai Hadiza Gabon kotu ne saboda ta ƙi auren sa bayan ya wahala da ɗawainiya.

Ya faɗa wa kotun cewa: “Zuwa yanzu na kashe N396,000 a kan ta. A duk lokacin da ta buƙaci kuɗi, haka na ke ba ta ba tare da wani ɓata lokaci ba tare da fatan za mu auri juna mu.”

Ita kuwa jarumar, tun tuni ta ƙaryata zargin ta hannun lauyan ta, Barista Mubarak Sani.

A cewar ta, ita ba ta ma taɓa ganin ko haɗuwa da Musa ba, kuma babu wata alaƙa ko kaɗan a tsakanin su.

Lauyan mai ƙarar ya gabatar da takardar lissafin kuɗin banki ga kotun kuma ya faɗa wa kotun cewa akwai wasu mutum huɗu da ya ba kuɗi a bisa iƙirarin sun kai wa wadda ake ƙarar.

Biyu daga cikin huɗun, wato Fatima Abdullahi ta ce ita ƙawar Gabon ce, shi kuma Abdullahi Yusuf, ya ce shi yaron ta ne. 

Sun amsa laifin su na yin sojan gona da sunan Hadiza Gabon har su ka karɓi kuɗi da sunan ta, amma sun roƙi kotun da ta yafe masu.

Bayan an fito daga kotun, lauyan wadda ake ƙara ya faɗa wa manema labarai cewa ya so kotun ta wanke Hadiza daga tuhumar tare da sallamar ta domin ba ta cuci kowa ko ta yi wa wani zamba cikin aminci ba, kamar yadda ake zargin ta.

Shi kuwa lauyan mai ƙara, cewa ya yi shi abin da ya ke so kawai shi ne a yi wa kowa adalci.

Loading

Tags: Bala MusaHadiza Aliyu GabonIsiyaku Abdulrahmankotun MusuluncilauyoyiMagajin Garizargin zamba
Previous Post

Kotu ta yanke wa Murja Kunya hukuncin sharar asibiti na tsawon mako uku

Next Post

MOPPAN ta Kano na so ‘yan Kannywood su tallafa wa ‘yan’uwan su da tarzomar zaɓen 2023 ta jawo wa asara

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Malam Misbahu M. Ahmad

MOPPAN ta Kano na so 'yan Kannywood su tallafa wa 'yan'uwan su da tarzomar zaɓen 2023 ta jawo wa asara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!