A YAU Babbar Kotun Musulunci da ke unguwar Hausawa Filin Hockey a Kano ta yanke wa jaruma Murja Ibrahim Kunya hukuncin sharar Asibitin Ƙwararru na Murtala har zuwa tsawon mako uku, ba tare da zaɓin tara ba.
Bugu da ƙari, za ta riƙa zuwa Hukumar Hisbah tsawon wata shida.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ruwaito labarin yadda aka gurfanar da jarumar da wasu mutum uku a kotun a bisa tuhumar wallafa bidiyon tsiraici a TikTok.
Hakan ya biyo bayan ƙarar ta da wata ƙungiya mai suna Zauren Malaman Kano ta kai ta.
An yi zama uku a kotun kafin komawar da aka yi a yau, inda aka yanke hukunci.
Bayan an karanto mata laifin da ake tuhumar ta aikatawa, nan take ta amsa laifin, wanda kan haka ne alƙalin kotun, Alhaji Abdullahi Halliru, ya yanke mata hukuncin.
A ɓangaren sauran waɗanda ake tuhuma, wato Aminu BBC, Ashiru Idris Maiwushirya da Sadiq Sharif, su ma an gabatar da su a kotu.
Bayan an karanto masu laifukan su, su ka amsa, su ma sai aka yanke masu hukuncin cewa za su riƙa sharar Masallacin Murtala har tsawon mako uku, ba tare da zaɓin tara ba.

Bayan hukuncin da aka yanke wa Murja Ibrahim Kunya da Aminu BBC da Ashiru Maiwushiriya da kuma Sadiq Sharif na ɗaurin talala tare da yin shara, a yanzu haka dai kotun ta na neman Ado Gwanja da Ummi Shakira domin su ma su karɓi nasu hukuncin bisa laifin da ake zargin su.
Lauyan ƙungiyar da ta kai su ƙara, wayo Zauren Malaman Jihar Kano, shi ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan fitowar sa daga kotun da aka zartar da hukuncin.
Ya ce: “A yanzu an yanke wa mutanen da ake zargi hukunci daidai da abin da su ka aikata. Don haka saura mutane biyu da su ka rage su ma su karɓi nasu hukuncin.”
Ya ƙara da cewa, “Mutane bakwai ne mu ka kai ƙara: Murja Ibrahim Kunya, Ashiru Idris (Maiwushiriya), Aminu BBC, Sadiq Sharif, Ado Gwanja, Ummi Shakira da kuma 442 wanda shi kuma a yanzu ya na can a Jamhuriyar Nijar a tsare bisa laifin da ya aikata a can ɗin.
“Saboda haka a yanzu za mu bi duk hanyar da za mu bi domin kawo Ado Gwanja da Ummi Shakira domin su ma su karɓi nasu hukuncin a gaban kotu.”