MAHAIFIN Mukhtar Hassan Hadi, matashin da jarumar Kannywood Hafsat Idris ta aura jiya, da ita kan ta jarumar, sun kira mujallar Fim a waya a yau sun bayyana cewa ba ɗan gidan marigayi Janar Sani Abacha ta aura ba.
A safiyar yau Fim ta samu labarin cewa Hafsat, wadda ake yi wa laƙabi da ‘Ɓarauniya’, ta yi aure jiya a asirce a Kano.
Wata ƙawar Hafsat ɗin, wadda ta buƙaci mu sakaya sunan ta, ita ce ta faɗa mana cewar ɗan gidan Abacha, wanda ba ta faɗi sunan sa ba amma ta ce “wanda aka haifa a Villa”, shi ne jarumar ta aura.
Ganin irin kusancin da ke tsakanin ƙawar da Hafsat, babu dalilin da zai sa mujallar Fim ta yi kokwanton labarin, musamman da ta ce Hafsat ɗin ce ta faɗa mata hakan da bakin ta.
Kafin wallafa labarin, mun nemi jin ta bakin Hafsat ɗin, amma hakan ya ci tura saboda ta kashe waya, sannan ba ta da niyyar zantawa da manema labarai a kan auren.
Sai dai ɓullar labarin ke da wuya sai Hafsat ta kira wakilin mujallar Fim a gigice ta faɗa masa cewa ita sam, ba ɗan gidan Abacha ta aura ba.
Ta faɗa wa wakilin mu cewa ta na so a gaggauta cire labarin daga gidan yanar mujallar.
Hafsat ta nuna cewa babban ɗan Janar Abacha, Alhaji Mohammed Abacha, shi ma ya damu kan lamarin.
“Mohammed ya fara magana, sai ku je ku cire shi,” inji ta.

Da wakilin mu ya buƙace ta da ta yi masa ƙarin bayani dangane da auren, sai ta nuna abin da ta ke so a rubuta, ta ce, “Ba ku san wanda Hafsat Idris ta aura ba, kawai kun yi ‘mistake’. Ku je ku cire shi,” inji ta.
Ta ƙara da cewa, “Babu wani bayani da zan ba ku… Ku je ku cire shi gaskiya tun kafin ya zama babban ‘issue'”.
Daga bisani, Hafsat ta hau Instagram inda ta faɗa wa jama’a cewa ba ɗan Abacha ta aura ba.
A saƙon da ta wallafa, jarumar ta ce, “Assalamu alaikum. Ina miƙa saƙon godiya na ga dukkanin masoya, ‘yan’uwa da abokan arziki na fatan alkhairi da su ka min. Sai dai ina son na yi magana a kan raɗe-raɗin da ke yawo, musamman ‘bloggers’ da ke ‘update’ a kai na, cewa mijin da na aura na da alaƙa da gidan Abacha. To wannan ba gaskiya ba ne, ba shi da alaƙa da su. Na gode.”
Shi ma mahaifin angon, wanda sananne kuma babban ɗan kasuwa ne a Kano, ya kira wakilin mu inda ya tabbatar masa da cewa ɗan sa ne Hafsat ta aura, ba ɗan Abacha ba.
Daga nan ya buƙaci a gyara labarin.
Sakamakon ƙurar da labarin ya tayar, mujallar Fim ta tuntuɓi ƙawar Hafsat ɗin nan da ta ba mu labarin cewa ɗan Abacha ne jarumar ta aura.
Sai ta ce, “Ba shakka ita ta faɗa mani. Sai dai ko ɗan ‘family’ ɗin su Abacha ta ke nufi, ba ɗan Abacha na cikin sa ba. Amma ba shakka ta ce ɗan gidan su Abacha ne. Saboda haka idan ma kuskure ne ko ƙarya aka yi, to daga gare ta abin ya samo asali.”
Mujallar Fim dai ta cire sunan gidan Abacha daga labarin farko da ta buga kamar yadda Hafsat da surukin ta su ka buƙata.