SAKATAREN Kwamitin Amintattu na Ƙungiyar Daraktoci (PROFDA), Ahmad Salihu Alkanawy, ya yi kira ga masu gudanar da harkar fim da su bi hanyoyin da ya kamata domin inganta harkar su ta hanyar rungumar juna da kuma fahimtar juna.
Alkanawy ya ce: “Akwai albishir da nake da shi kamar guda biyu zuwa uku, wanda kamar yadda wasu daga cikin ‘yan fim sun sani a kwanaki mun yi zama a kan matsaloli da ake fama da su, wanda mun gano duk iyawar ka da tuƙin mota da ƙwarewar ka, idan aka ba ka tsohuwar mota aka ce ka tuƙa, tafiyar ba za ta yiwu ba.
“To mu ma haka abin yake. Duk yadda aka kai ga koya wa mutane fim, idan babu kuɗi to babu magana, domin an koya maka aiki da kayan zamani ka iya amma tsakanin ka da kayan aikin sai dai ka ajiye.
“Saboda haka muna ta ƙoƙarin yadda za a yi a samu kuɗin da za a samu kowa ya yi fim ɗin da ya kamata.
“Ba a canza mota ba, ba a sayi babbar waya ba, ba a ƙara aure ba, a’a, ana maganar a gina ita masana’antar.
“Kuma kamar yadda Shugaban Hukumar Tace Finafinai, Abba El-Mustapha, yake tare da mu, Mataimakin Gwamnan Kano ya kira mu a kan yadda za a samu tagomashi na kuɗaɗe daban-daban da suke a ƙasar nan wanda mu ba ma samu. Kuɗin da za a samu ba wai ɗan kaɗan ba ne, don haka duk waɗanda suke da cibiyar horaswa ta fim a Kano za su samu kuɗi na wannan horaswar.”
Daraktan ya ci gaba da cewa, “Sannan abu na biyu kamar yadda muka ga mutanen Chana sun ware kuɗi sun samar da wani ɗan ƙaramin talbijin na dirama, wanda a yanzu suna da kuɗin da sun fi Nijeriya, wanda ko mu ma za mu iya yi. To in-sha Allahu za mu je wannan matakin. Amma dai babban abin da yake akwai shi ne haɗin kai kamar yadda aka ce.
“Kuma sannan mu daina damuwa da idan an ce nan wajen ba ku yi daidai ba, don haka mu fi damuwa da mu ji sukar fiye da yabo.
“Shi ya sa aka ce wasu daga cikin malamai na can baya, idan suka rubuta littafi, sai su bincika su ga a cikin malamai waye yake yin adawa da su su kai ya duba don ya fito da sukar.
“Don haka mu rinƙa karɓar gyara kuma mu yarda za a soke mu.”