SHUGABA Bola Ahmed Tinubu ya bayyana mutuwar shahararren ɗan wasan kwaikwayo ɗin nan Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja) a matsayin babban rashi ga ƙasar nan, saboda ɗimbin gudunmawar sa ga cigaban ta.
Mujallar Fim ta ba ku labarin cewa Samanja, wanda tsohon soja ne kuma ma’aikacin gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, ya rasu ne a shekaranjiya Lahadi, ya na da shekaru 84 a duniya.
A saƙon da ya aika wa iyalan mamacin a yau, wanda aka raba wa manema labarai, Tinubu ya yi masu ta’aziyyar wannan babban rashi da aka yi.
A saƙon, wanda mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai, Cif Ajuri Ngelale, ya rattaba wa hannu, Tinubu ya bayyana rasuwar a matsayin wani al’amari mai ƙona rai, ya ce marigayin ya bada gudunmawa ga ƙasar nan ta hanyar abubuwa daban-daban da ya yi a rayuwar sa.
Tinubu ya ce: “Marigayi Pategi ya zaɓi ya taimaka wa ƙasa ne a daidai lokacin da ƙasar ke buƙatar sa. Shirin sa na ‘Samanja’ ya wajabta ga kowa a matsayin abin kallo don samun nishaɗi a tsawon shekaru masu yawa.
“Ta hanyar shirin, ya koyar da matasa tarbiyyar son ƙasa tare da girmamawa ga sojojin mu. Mutum ne ɗan kishin ƙasa wanda ya bar ɗimbin abubuwan da za a riƙa tunawa da shi.”
Shugaban ƙasar ya hori iyalan Samanja da al’umma da gwamnatin Jihar Kwara da Majalisar Masarautar Pategi da dukkan masu harkar nishaɗantarwa na Nijeriya da su yi la’akari da abin farin cikin da marigayin ya bari na ayyukan sa abin yabo.