TSOHON ɗan wasan kwaikwayo ɗin nan, Malam Abdullahi Shu’aibu (Ƙarƙuzu ko Abdu Kano), ya yi kira ga jama’a da su kawo masa ɗauki bayan ya makance sannan ya na fama da matsanancin rashin lafiya.
Bugu da ƙari, ba ya da kayan abinci.
Ƙarƙuzu ya yi wannan bayanin ne a wata hira da kafar yaɗa labarai ta ‘Zinariya TV’ ta yi da shi, wanda bidiyon ta ke ta yawo a soshiyal midiya.
Mujallar Fim ta kalli hirar, kuma ta ruwaito cewa don a tuno da kirarin da Ƙarƙuzu ya ke yi a wasan kwaikwayon da ya riƙa yi a shekarun 1980, ɗan wasan ya ce, “Ni dai ni ne Ƙarƙuzu, ɗan Ƙurmuzuzu, jikan Ƙuzu na Bodara, abar ni sai ta Allah ta yi.”
Ya ci gaba da cewa, “Ni dai suna na Abdullahi Ƙarƙuzu, amma al’amura yadda su ke, suna na Abdullahi Shu’aibu, kuma ana kira na da suna na Abdullahi Kano; waɗannan duk suna na ne. Halin da na ke ciki a yanzu, wato a wuri na mai kyau ne, a wurin Allah ma mai kyau ne. Amma ba na jin daɗi.
“Saboda yanzu shekara na 43 ina wannan al’amura. Amma gaskiya, yanzu wani lokaci sai in kwana ba ni da abin da za a ci a gida na. Kuma wani abin tausayi, ni Ƙarƙuzu a yanzu zancen da na ke, wannan gida da na ke ciki an sa shi ma a kasuwa, ba gida na ba ne, haya na ke yi.
“A yanzu a cikin wannan al’amari da na ke yi, yanzu in an ce na mallaki gida mai ɗimbin yawa, waɗansu da za su ke kallo na sai su ce gaskiya ne. Amma wallahi tallahi, ɗaki ɗaya a ce nawa ne wanda na mallaka, ba ni da shi.
“A cikin wannan aiki da na ke da wannan shekara, na makance. Yanzu zancen da na ke mai kallo na ba na gani, ni sai dai ya gan ni, amma ni ba na ganin sa. Ba na gani, idon ya makance. An yi aiki a wannan idon (dama), bai gani ba, aka zo aka sake yi a wannan idon, bai gani ba. Daga ƙarshe daktoci sai su ka gaya min wai akwai wata cuta, hawan jiki gilakoma, su kuma daktoci sun riga sun yi ƙiyasin cewa wannan idon ba zai gani ba, ‘Ƙarƙuzu sai dai ka haƙura haka’.”
A kan batun ‘yan fim da za su iya taimaka masa, irin su Ibrahim Mandawari, sai ya ce: “Ai duk daga baya kenan. Su kuwa, su Mandawari ai daɗaɗɗu ne a gare mu. Kuma waɗanda mu ke maganar sun mutu. Kamar na jihohi, kamar dai a Kano, akwai Karo-Da-Goma, akwai Malam Mamman, waɗanda mu ka yi aikin da su, duk an rasu tsofaffi.
Ya yi nuni da cewa taimako gare shi zai iya zuwa daga ko’ina. Ya ce, “Ai yanzu ba wai al’ummar Kano kawai ko al’ummar Jos ko na Kaduna ko na Legas ba, duk al’ummar duniyar nan ina buƙatar a taimaka min. Wannan gida yanzu da aka sa shi a kasuwa za a sayar, ba ni da kuɗi, bayan ba ni da kuɗi ba na gani, ba na zuwa ko’ina. Ina da ‘ya’ya. Maganar abinci kam ma babu. Wannan shi ne zahirin gaskiya.
“To, kuma yau ɗin nan, yau yadda ta ke, sai an daure. Duk abin da za a yi mini, na san abin da za a yi mini abu ne wanda in Allah ya so ya yarda sadaƙatujjariya ne.
“Bayan an yi min, za kuma ka je ka samu abin da ka ke nema a inda za ka tafi lahira ka je ka kwanta.
“In-sha Allahu, ina neman wannan taimako a taimake ni. Ko ba wannan gida ba ma da na ke ciki, ni dai in samu abin da zan ɗan gangara lahira; in na tafi gidan da za a zo a ce wannan gidan wane ne, taimaka masa aka yi ya saya.
“Kuma a tallafa min da kayan abinci. Bayan kayan abinci, a tallafa min da ɗan abin da zan samu ina rufewa. A taƙaice dai ba na gani, ba ni da lafiya, ga shekaru masu yawa.
“Saboda haka, wannan abin da na ke magana, duk wanda ya ke da niyya zai taimaka min, a’a miliyan goma ne, miliyan biyu ne, miliyan ɗaya ne, naira hamsin ne, naira ɗari ne, a taimaka min ta kan account bidiyon da ku ke kallo yanzu, Fisabillahi, masu hannu da shuni, su ke bai wa majinrarai.”
A wani ɓangaren kuma, kafa yaɗa labarai ta Dokin Ƙarfe TV ta ba da labarin cewa shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Nijeriya ɗin nan, Ahmad Musa, ya ba Ƙarƙuzu taimakon kuɗi N500,000, sannan kuma ya ba da umarnin a nemo gida ya saya masa, wanda bai wuce naira miliyan huɗu zuwa biyar ba.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa a halin yanzu jama’a sun zuba ido su ga irin rawar da ‘yan Kannywood za su taka a game da halin da abokin aikin nasu ke ciki.
Ga lambar asusun bankin Ƙarƙuzu:
Lambar asusu: 3034702720
Banki: First Bank
Sunan asusu: Shu’aibu Abdullahi.