MALAM Kabiru Musa Jammaje ya yi fice wajen shirya finafinai na Turanci a Kannywood. Amma an daɗe ba a ji ɗuriyar sa ba. Sai dai kuma kwanan nan ya yi aikin shirya sabon fim ɗin sa mai suna ‘Princess of Galma’. Don haka ne mujallar Fim ta tattauna da shi a game da aikin fim ɗin, da kuma inda ya sa gaba.Ga tattaunawar:
FIM: Ka ɗauki dogon lokaci ba ka shirya fim ba sai a ‘yan kwanakin nan da ka yi aikin sabon fim ɗin ka mai suna ‘Princess of Galma’. Mu na so ka yi wa masu karatun mu ƙarin bayani.
KABIRU JAMMAJE: To, ka san shi aikin fim ba wani abu ne mai sauƙi ba, ana shan wahala sosai wanda zai kasance ko barci ma ba a samu a yi. Kuma kuma cikin yardar Allah a wannan aikin mun yi shi a cikin sati biyu mu ka gama. An gama cikin nasara, komai ya tafi daidai. Kuma ba mu ɗauki fim ɗin da gaggawa ba, mun bi shi a hankali ta yadda za a samu abin da ake so. Kuma dole na jinjina wa shi daraktan, Galadima Muhammad, shi da wanda ya taimaka mini, wato furodusa ɗin, da sauran dukkan ma’aikata da jarumai, su ma sun yi rawar gani sosai.
FIM: Yanzu kuma ina aka sa gaba?
KABIRU JAMMAJE: To a yanzu mu na mataki na tacewa, wato tace hotunan da kuma harhaɗa su, wanda kuma daga baya a zo a saka sauti da sauran su, zuwa gaba kuma a sake shi in-sha Allah.
FIM: Shi wannan fim, kamar yadda ka saba sakin fim ɗin ka a baya ne za ka sake shi ko akwai wani tsarin da ka yi?
KABIRU JAMMAJE: Finafinai da mu ka yi, na farko dai mun buga sidi ne mu ka kai kasuwa, saboda a lokacin kasuwar sidi ta na ci. Na baya kuma da su ka fito sai mu ka kai su sinima. To amma shi wannan ya zo ne da wani sabon salo, domin akwai taro da mu ka fara a shekarar da ta gabata mai suna Ranar Jammaje, wato ‘Jammaje Day’. Wannan rana ce da ɗaliban Makarantar Jammaje su ke haɗuwa su yi zumunci, kuma a kira malamai su yi jawabai wanda duk ɗaliban ne na ƙasa su ke zuwa. Kamar yadda mu ka yi taron bara a watan Disamba, a bana ma haka za mu yi wanda zai kasance a ranar 26 ga Disamba, 2023 a sabuwar Jami’ar Bayero, a babban ɗakin taro na Musa Abullaahi. Kuma a wannan ranar za mu nuna fim ɗin. Kuma ba wai kawai ɗaliban ne za su shiga su kalla ba, har da sauran jama’a masu sha’awar kallon finafinai za su iya zuwa a ranar, su ma su kalla.

FIM: Shi wannan sabon salon, wani yanayi ne ya bayar da hakan, ko dai dabarar kasuwa ce?
KABIRU JAMMAJE: To, zan iya cewa dabarar kasuwar da kuma tafiya da zamani a harkar kasuwanci. Domin ka ga a baya akwai sinima a nan Kano a cikin Kantin Shoprite. To kuma a yanzu an rufe ta. Wannan ya sa na yi tunanin samar da wani tsarin don ganin harkar ta samu mafita, don haka sai na ga wannan sabon tsarin zai iya samar wa da masana’antar Kannywood mafita, don haka sai mu ka ga samar da majigi a nuna fim ɗin abu ne mai sauƙi yadda mutane za su zo su kalla, idan har buƙatar mu ta biya, harkar ta samu karɓuwa. Ka ga sai wasu ma su biyo mu, wanda kuma mu na sa ran daga wannan waje za mu ci gaba da samar da wuraren da za a ci gaba da nunawa. Don haka wannan dama ce ga waɗanda su ka daɗe ba su kalli fim ba su zo su kalla. Kuma mu na fatan kuɗin da mu ka kashe a lokacin ya dawo, domin ka ga shi ɗakin taron mutum dubu ɗaya ya ke ci, to ka ga idan mutane dubu su ka kalla, wasu dubu ɗin su ka ƙara shiga don su kalla, don taron na wuni guda za mu yi. Kuma da man kamar yadda na faɗa maka wannan gwaji ne, kuma da man tun tuni ya kamata mu samar da namu tsarin. Domin ita sinima tsarin ta ya na da wahala ka je ka yi ta tallace-tallace, kuma bayan ka nuna fim ɗin ma za ku raba kuɗin biyu ne. Ka ga wannan kuma babu wannan. Saboda haka ni wani abu ne da na ke ganin na ƙirƙiro, wanda na yi amfani da basira ta ne. Don haka idan mun riƙe ta, zai zama wata kasuwa ce aka samar sabuwa wadda za a rinƙa amfani da ita a finafinan mu na gaba. Kuma tun da ana buƙatar kasuwar ya na da kyau masu fim su kwaikwaya. Domin ka ga bayan nan Kano za mu nuna shi a Kaduna duk a irin wannan tsarin, ta yiwu ma har da Abuja. Wanda idan mun kammala ne za mu tafi zuwa mataki na duniya kamar Amazon da sauran su, daga nan sai gidajen talbijin manya; sai kuma matakin ƙarshe, shi ne mu kawo shi Arewa24. Sai kuma You Tube, ko da yake ni ba ni da ra’ayin saka fim a YouTube don ba ya burge ni.
FIM: Idan har aka kai ga hakan, ka kai ga cimma burin ka kenan?
KABIRU JAMMAJE: Ina ganin hakan kenan, domin ni buri na shi ne isar da saƙon zai wayar da kai a kan yare da kuma al’adun ƙasar Hausa. Duk da yake finafinan da na ke na Turanci ne, amma dai ina yi ne yadda tsantsar al’adun Hausa domin isar da shi a duniya. Wannan ya sa za ka ga na fi ɗaukar labarin sarautar ƙasar Hausa. Don haka a yanzu ma akwai finafinai da zan yi aikin su bayan fitowar ‘Princess of Galma’ domin sha’awa da ƙara fito da al’adun mu na ƙasar Hausa, don yawancin finafinan mu (na Kannywood) sun fi bayar da labarin soyayya. In ban da a baya da kamfanin Sarauniya ya yi fice a finafinan gargajiya, duk soyayya ta fi yawa. To ina ganin duk da babu su yanzu, ni zan zama madadin su saboda na ɗauko wannan layin zan ɗora daga inda su ka tsaya. Don haka masoya kallon finafinan Kannywood da na Jammaje Productions sai ku yi tururuwa ranar 26 ga Disamba, 2023 domin kallon fim ɗin ‘Princess of Galma’ a BUK; ɗakin taro na Musa Abdullahi a nan za mu haska shi.
FIM: To madalla, mun gode.
KABIRU JAMMAJE: Ni ma na gode.

