A YAU Asabar, 12 ga Nuwamba, 2022, aka ɗaura auren matashin marubuci a Kannywood, Najib Abdulazeez Adam, wanda aka fi sani da Najib Marubuci, da sahibar sa Khadija Abdulkareem Yakub.
An ɗaura auren da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ƙofar gidan baban amarya, Malam Abdulkareem Yakub, da ke Tsohon Gari, Tudun Shuni, Tudun Wadan Ɗankadai, a Jihar Kano a kan sadaki N30,000.

Ɗaurin auren ya samu halartar ‘yan fim irin su Abdul M. Shareef, Sani Hamza Funtua, Nasiru Ali Ƙoƙi, Muftahu Lawal Getso, Haruna Gidaje, Abdul S.D., Abdul Zifa, Babangida D. Gumzak, Shamsu Shatan Turaki da sauran su.
A mata kuma akwai Maryam Malika, Fanan, Fauziyya, Rumasa’u da Bilkisu.
A jiya Juma’a an yi dina a ‘Ɗansarki Event Centre’ da ke Tudun Wadan Ɗankadai.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.
