A RANAR Talata, 10 ga Disamba, 2019, wanda ya zo daidai da ranar murnar zagayowar ranar haihuwar ta, shahararriyar jaruma kuma furodusa Rahama Sadau ta ƙaddamar da wani gida mai suna ‘Sadauz Home’ wanda ya ƙunshi dukkan kamfanonin ta. Kwanaki kaɗan da yin hakan, sai ta yi tattaunawa ta musamman da mujallar Fim a kan sabon wajen da ta buɗe da kuma batun halin da harkar fim ke ciki, da batun yaushe za ta yi aure, da batun masu sukar ta a soshiyal midiya, da alaƙar ta da Sadiq Sani Sadiq da mawaƙin nan Akon. Ga yadda hirar ta kasance:
FIM: Mu na taya ki murnar buɗe gidan abinci da ki ka yi. Me za ki ce game da wannan gagarumar nasara da ki ka samu ta buɗe ‘Sadauz Home’?
RAHAMA SADAU: Assalanu alaikum. Alhamdu lillah, na gode sosai, Allah ya saka da alheri. Kuma ni na fi kowa farin cikin buɗe wurin nan sai suna ‘Sadauz Home’, saboda wuri ne da na daɗe ina mafarkin buɗe shi. Kamar yadda mutane su ka sani, ina ‘different businesses’ masu sunan Sadau; akwai ‘Sadau Pictures’, ‘Sadau Beauty’, ‘Sadau Lip Stick’… Sadau, Sadau ɗin ya yi yawa! Sai na ga cewa bai kamata a ce na rarraba kowane Sadau, Sadau da ‘different’ shaguna ko wurare ba. Kawai sai na samu ƙaton gida, wanda na ɗauki duk wani abu da ya danganci Sadau na yi shi a cikin gidan, shi ya sa na ke kiran gidan ‘Sadauz Home’.
Idan ka zo ‘Sadauz Home’ ɗin, za ka ga akwai wurin aski, ‘beauty lounge’, akwai ‘saloon’ na mata, akwai wurin abinci, akwai abubuwa da dama waɗanda su ka dangance ni. Shi ya sa na ke kiran shi ‘Sadauz Home’.

FIM: Mata ‘yan shagunan saida kayan sawa na mata da jakunkuna su ke yi, amma sai ga shi ke kin ware daga cikin su kin buɗe gidan abinci. Me ya ja hankalin ki?
RAHAMA SADAU: Gidan abinci ba wani ‘ambition’ ba ne da na ke da shi da daɗewa ba. Amma duk wanda ya san ni ya san da daɗewa na ke da situdiyo, na ke ‘makeup’ da ‘saloon’. So sister na ta iya abinci, ‘chef’ ce, sai na ga cewa da mu raba ‘businesses’ ɗin , me zai hana mu haɗa su wuri ɗaya, ko da yaushe mu na wurin. Abin da ya fara jawo hankali na kenan. Ɗayan ƙanwa ta ta na ‘makeup’, ɗayar ta na abinci, ni kuma ina da ofis ‘Sadau’s Pictures’, kawai sai na ga a haɗa su a wuri ɗaya. Abin da ya fara kawo wannan tunanin kenan.
FIM: Waɗanne irin abinci ku ke yi a wurin? Na gargajiya ne ko ‘continental’?
RAHAMA SADAU: Mu na yin na gargajiya, su tuwo, masa da duk sauran abincin gargajiya ana yi. In ka juya kuma, ƙanwa ta ta na yin ‘continental’ irin abincin ‘yan Chana, Potigis da duk dai abincin su na ƙarya! (dariya)
FIM: Rahama Sadau ta na ɗaya daga cikin ‘yan fim ɗin da duk abin da ta yi ya kan zama abin surutu a gari, musamman a soshiyal midiya. Kwanan nan kin ɗora wasu hotunan ki a shafukan ki na Instagram da Facebook, wanda su ka zama abin ce-ce-ku-ce. A duk lokacin da ki ka tsinci kan ki cikin irin wannan yamaɗiɗin ya ki ke ji a ran ki?
RAHAMA SADAU: Wallahi mutane ke jin surutun, ba ni ba. Kamar yadda ka ke magana, haka jiya wani ya zo ya na tambaya na, har ya ke cewa in faɗa masa inda na ke samun ‘courage’ da har ya ke gani na ina dariya. Ni ba na gani, mutane su ke gani! In mutum miliyan za su yi magana, wallahi ba na gani. Saboda da na ɗora abu na ke yin gaba. Saboda yadda na riga na ɗora wa kai na, duk abin da ka yi wallahi sai an yi magana a kai. Yau idan hijabi na saka a jiki na, wallahi sai an yi magana a kai. So, kawai ‘just be yourself’, shi ne.
Magana ne da ba daɗewa za a yi ba an daina yin shi, an ɗauki wani kuma an ɗora a kai. Ba wani abu da yanzu mutane su ka ɗauke shi da muhimmanci sama da magana: wannan ya yi magana, wancan ya yi magana. Ni ba na ma ɗaukar shi wani abu; da na yi, na wuce.
FIM: Wane kira za ki yi ga masu irin wannan halin na damuwa da abin da bai shafe ka ba?
RAHAMA SADAU: ‘Opinion’ ne, ‘opinion’ ni na ɗauke shi. Kuma soshiyal midiyan da ka ke magana, ‘Instagram standard’ ne, a wurin ne kawai za su yi magana. Babu wanda zai zo ya tare ka ‘face-to-face’ ya yi maka magana, bai isa ba wallahi! Iyakar sa fa Instagram, to me zai dame ka?
Kawai dai abin da na ke so a gane, shi fa mutum kowa da rayuwar sa, kowa da ‘choice’ ɗin sa, kowa da irin abin da ya ke so a rayuwa. Ni ba zan iya sa maka ra’ayin son kaza ba, kai ma ba za ka iya sa mani ra’ayin son kaza ba. Don haka in ka yi magana a kai na, ra’ayin ka ne ka ji ka na so ka yi; in ka zage ni, ra’ayin ka ne. Don haka na ce kowa ya na da ‘opinion’, kuma ‘everybody’s opinion should be respected’. Amma irin waɗannan abubuwan da ke faruwa, gani na ke akwai ‘issues’ da dama da su ka fi wannan. A wuri na ɓata lokaci ne ka tsaya ka na maganar wani.
FIM: Menene matsayin Rahama Sadau a Kannywood?
RAHAMA SADAU: Matsayin Rahama Sadau! Rahama Sadau ta na nan a matsayin jaruma. (dariya)
FIM: Yanzu kin rage fitowa a finafinai. Menene dalili?
RAHAMA SADAU: E to, gaskiya idan mutum ya duba shekara ɗaya zuwa biyu da su ka wuce, karatu ne ya ja haka. Sai kuma aka gama karatu aka kalli wani ɓangare na rayuwa. Amma ba daina fim ɗin na yi ba, har yanzu ana ɗan taɓawa, kawai abubuwan ne sun yi yawa. Yanzu Rahama Sadau ta koma saida tuwo-tuwo! (dariya) In ka juya za ka ga sati mai zuwa ma ina da aiki da zan tafi.
Don haka abubuwan ne kawai dole sai an yi ‘balancing’, ba irin da ba ne da ko da yaushe ka na da aikin fim, ka na fita fim. Gaskiya ba haka ba ne.
FIM: Ya maganar finafinan Kudu na Nollywood?
RAHAMA: Gaskiya na fi yin finafinan Kudu ma ni yanzu a kan Kannywood.
FIM: Ina batun Hollywood kuma?
RAHAMA SADAU: Heyyyy! Allah Ya kai mu. (dariya) Babu wanda ba ya son zuwa.
FIM: Ya maganar aikin da ki ka yi da su mawaƙi Akon a Amerika?
RAHAMA SADAU: Mun yi aiki da shi ƙwarai. Ni ma bai daɗe ba da na tambaya me ya samu aikin har yanzu? Kuma ka san ‘process’ ɗin Hollywood da namu daban ne, sai a kai shekara biyu a ɗaukar shiri, ballantana a zo maganar editin da wasu abubuwa, sai da aka yi shekara biyu a ɗaukar fim ɗin nan. Ban sani ba sun gama ko ba su gama ba, ban dai ƙara dubawa ba. Amma dai na san ko za a daɗe fim ɗin zai fito. Amma na ga sun fara ‘teaser’.
FIM: Menene maganar da ake cewa ku na soyayya da Sadiq Sani Sadiq?
RAHAMA SADAU: (dariya) E to, akwai soyayya ta ‘yan’uwantaka tsakani na da shi, amma ba soyayya irin wadda mutane ke tunani ba. Gaskiya Sadiq aboki na ne, ba ni da aboki kamar shi a masana’antar fim. Mutum ne da tamu ta zo ɗaya, shi ne kawai dalilin da ya sa. Babu maganar soyayya ko aure ko wani abu. Hotunan da mu ka yi, na fim ne kuma mutane sun ga fim ɗin.
FIM: Ya ki ke ganin tafiyar wannan wuri da ki ka buɗe da harkar fim kuma? Ba ki ganin cewa ɗaya zai danne ɗaya?
RAHAMA SADAU: Gaskiya ba ɗaya ba ne. Ba zan iya cewa wannan ya fi wannan wahala ba, amma sana’ar fim komai wahala. Amma kuma ɗan kallo ba zai gane ba, saboda cikin awa ɗaya ya gama kallon fim ya tashi ya tafi. Ka ga ba ɗaya ba ne. A nan akwai manaja, sannan akwai ‘operator’ da za ta riƙa ‘operating’; ƙanwa ta Zainab ita ke ganin komai, don haka wahalar ya ɗan ɗauke mani kaɗan. Duk da cewa sabon wuri ne, dole sai na ɗan zauna na wani lokaci, saboda wani zai zo wurin ne kawai don ya ga Rahama, da abubuwa makamantan haka.
FIM: Akwai lokacin da ki ka yanke a ran ki da za ki bar harkar fim?
RAHAMA SADAU: Gaskiya babu wani lokaci da na ɗaukar wa kai na zan bar harkar fim. Ban ma sa wa rai na haka.
FIM: Ina maganar aure?
RAHAMA SADAU: An kusa (dariya) … idan mijin ya zo!
FIM: In na fahimce ki, Rahama Sadau a kasuwa ta ke kenan?
RAHAMA SADAU: Gaskiya in da mai so ya zo ya ɗauka! (dariya)
FIM: Kannywood a wannan shekara ta 2019, ci-gaba aka samu ko ci-baya?
RAHAMA SADAU: Gaskiya babu maganar ci-gaba a masana’antar fim a wannan lokacin da mu ke ciki. Saboda idan ka duba gaba ɗaya idan furodusa ya yi fim a wuri ɗaya ya ke iya saida fim ɗin sa – siniman Kano. Mu na da jihohi 19 a Arewa, kuma duk su na kallon fim. A wani lissafi da aka yi, an fi kallon finafinan Hausa a kan na Kudu. Amma wannan kasuwar ta lalace, sinimar kawai ake iya kallon fim. Shin fim ɗin da ka yi ɗan Kano kawai ka yi ma wa? Ina sauran jihohin da su ma su na da buƙatar kallo? Idan ba ku manta ba, na yi ‘Rariya Tour’; in ka ga mutanen da su ka zo su ka kalla… mun je Yola, mun je Gombe duk mun nuna, amma saboda rashin gidajen kallon ba a kai masu finafinai. Yanzu sai dai ka yi fim kawai ɗan Kano ya kalla. Don haka ka gaya mani ta inda ci-gaba ya ke. Wanda a da kai ka san idan ka yi fim ka buga sidi da fim ɗaya sai ka yi kuɗi. Ban da yanzu saboda kowa ja baya ya ke yi, babu wanda zai zuba kuɗin sa ya yi fim, kuɗin su ƙi fitowa.
FIM: Wace shawara za ki bayar ta yadda za a shawo kan wannan matsala?
RAHAMA SADAU: Kullum in mu ka zauna mu na magana, na kan ce dole sai mun haƙura mun tafi ‘digital’, kamar yadda duniya ta tafi. Idan ba za a yi ‘providing’ sinimu da yawa ba, a yi ko da guda biyar ne a garuruwan da aka san cewa sun fi kallon finafinan Hausa.
Idan kuma ba za a yi wannan ba, sai dai mu tafi ‘digital’. Saboda duk furodusan da na haɗu da shi, sai na tambaye shi, “Ka na da dibidi a gidan ka?” Bai da shi! Kowa a waya ya ke kallo. Sai a nemi hanyar da za a tafi ‘digital’ ɗin da ɗan kallo zai sa a wayar shi ya kalla. Wannan shi kaɗai ne mafita.
In kuma ba za a iya wannan ba, gwamnati ta yi haƙuri, ta daure – saboda mu na biyan haraji, babu kamfanin da zai yi fim bai biya haraji ba, duk da ban dai sani ba, amma ni ina biya – a daure a gina mana sinimu ko da guda biyar ne a gani, a ce yau wancan ya saida dubu biyar a Kano, ana yi maka maganar miliyoyi ne. Wannan shi ne mafita, in ba shi ba sai dai a haƙura.
FIM: A ƙarshe, me za ki ce wa masoyan ki?
RAHAMA SADAU: Masoya mun gode da soyayya. (dariya) Sannan kuma a ci-gaba da haƙuri da mu. Mun gode sosai.
