KAMAR yadda ya saba, shahararren mawaƙin siyasa Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) ya raba wa mutanen ƙauyen su Kahutu kayan abinci da kuɗin cefane don rage masu raɗaɗin rayuwa da ake ciki.
Mai taimaka masa a ɓangaren soshiyal midiya, Rabi’u Garba Gaya, bayyana cewa, ” Mai girma shugaban ƙasar mawaƙa, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), ya tallafa wa mutane dubu goma da kyautar kayan abinci. Sannan kuma ya ware N50,000,000,00, ya ba kowanen su N5,000, domin su yi cefane.

Mujallar Fim ta ruwaito cewar Rarara ya yi taron rabon ne a garin Kahutu da ke Ƙaramar Hukumar Ɗanja ta Jihar Katsina.
Lokaci zuwa lokaci mawaƙin na yin irin wannan rabon don tallafa wa mutanen garin na su.
