WASU daga cikin sanannun ‘yan masana’antar finafinai ta Kannywood, ciki har da Ali Nuhu da Nazir Adam Salih, sun mayar da martani ga fitacciyar ‘yar wasa Hajiya Ladin Cima a kan iƙirarin da ta yi cewa wai ba a taɓa biyan ta ladar sama da N5,000 ba a duk shekarun da ta yi ta na wasan kwaikwayo.
Ladin Cima (Tambaya) ta jawo fushin ‘yan fim da dama bayan ta yi ƙorafi game da yadda wasu furodusoshi su ke biyan ta ladar aikin fim.
Ta yi ƙorafin ne a cikin wata hira da ta yi da shirin “Daga Bakin Mai Ita” na BBC Hausa, wanda gidan rediyon ke wallafawa a soshiyal midiya.
Lokacin da BBC Hausa su ka tambaye ta abin da ya sa ba ta tanadi komai ba ganin cewa ta daɗe ta na wasan kwaikwayo, jarumar ta ce, “Ai ni tun da na fara fim kawo yanzu ban yi fim ɗin da za a ɗauko naira dubu hamsin ko dubu ashirin a ba ni ba, bare in yi tanadin wani abu.
“Da na je fim ɗin nan, za a ba ni dubu biyar, dubu uku, dubu huɗu. Yanzu yau ɗin nan na je shutin, wallahi dubu biyu aka ban.”
Wannan magana ba ta yi wa ‘yan fim daɗi ba, musamman ganin yadda ta tada ƙura a soshiyal midiya, musamman a Facebook, inda mutane da dama su ka yi wa ‘yan fim caa da cewa abin da su ke yi wa ‘yan wasa irin su Tambaya zulunci ne.
Akwai ma waɗanda su ka ce to a ina marasan matan industiri ke samun kuɗaɗen da su ke fantamawa da su?
Marubuci kuma furodusan shirin ‘Gidan Badamasi’ mai dogon zango, wanda tashar Arewa 24 ke nunawa a duk ranar Alhamis, Nazir Adam Salih, ya maida mata da martani da cewa, “Na biya Ladin Cima (Tambaya) dubu arba’in a fim ɗin ‘Gidan Badamasi’ kashi na uku; na sake biyan ta dubu talatin a kashi na huɗu. Haka nan ko wata ɗaya ba a yi ba na sake biyan ta naira dubu talatin a wani ɗan bidiyo na faɗakarwa, kuma a duka ba ta yi fitowa sama da goma ba.
“Haka nan mun yi gyaran ‘scene’ guda wanda magana kawai ta yi, mu ka biya ta dubu biyar, mu ka kuma sai mata abinci na dubu kusan huɗu a wuni guda.
“Haka nan a gaba na Hadiza Gabon ta ba ta dubu ɗari biyu da saba’in kyauta! Amma duk da haka ka ji halin ɗan’adam. Kai jama’a!!”
Haka kuma a wani hoton allo da KB 2-Effects ya ɗora a shafin sa na Instagram, inda ya nuna cewa wani mawaƙi mai suna Sabon Shata ya yi wa fitaccen jarumi Ali Nuhu magana a Instagram, ya ce masa, “Ka na ina?” Sai Ali ya ce masa, “Ga ni nan. Ka je ka tambaye ta ko nawa aka biya ta a ‘Alaqa’? I do not know why some of the elderly people keep betraying the industry just to gain people’s sympathy. Amma Allah ai ya na gani, kuma zai hukunta wanda ya zalunci wani.”
Ali Nuhu ya na ɗaya daga cikin mutanen da a industiri ya ke ƙoƙarin biyan dukkan wanda ya yi masa aiki da kuɗi masu tsoka.