A RANAR Asabar mai zuwa za a yi taron rantsar da sababbin shugabannin Ƙungiyar Jaruman Kannywood ta Jihar Kaduna (Actors Guild).
Don haka ƙungiyar, wadda ke ƙarƙashin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), ta bayyana cewa ta na gayyatar ‘ya’yan ta da sauran masu ruwa da tsaki na industiri zuwa wurin rantsarwar.
A cikin sanarwar da ya bayar, sabon kakakin ƙungiyar, Isah Man United, ya ce, “Ƙungiyar ‘Actors Guild’ Kaduna, ƙarkashin jagorancin sabon shugaban ƙungiyar, Zaharaddin Sani Owner, na farin cikin gayyatar ‘yan’uwa da abokan arziki zuwa wurin taron rantsar da sababbin membobin ta.”
Za a gudanar da taron ne a ranar Asabar, 12 ga Fabrairu, 2022 a ɗakin taro na NUT da ke Mogadishu Layout, Kaduna, da misalin ƙarfe 10:00 na safe.
Kakakin ya ƙara da cewa akwai manyan baƙi da aka gayyata, waɗanda su ka haɗa da Yerima Shettima, Dakta Muktar Ramalan Yero, Hon. Usman Mafi-Mishkila, Hon. Hussaini Kero, ASP Hamza, ASP Muhammad Jalige, Abdul Amart Maikwashewa, Adam A. Zango, Rahama Sadau, Hadiza Gabon da Abdul M. Shareef.
![]()







