• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rasuwar daraktan ‘Izzar So, Nura Mustapha Waye, ta girgiza Kannywood

by DAGA ABBA MUHAMMAD
July 3, 2022
in Labarai
0
Marigayi Nura Mustapha Waye

Marigayi Nura Mustapha Waye

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN wayi gari a yau da baƙin labarin rasuwar Malam Nura Mustapha Waye, daraktan fitaccen shirin nan mai dogon zango mai suna ‘Izzar So’.

Nura ya rasu ne a safiyar yau Lahadi, 3 ga Yuli, 2022, da misalin ƙarfe 8:00 na safe a wani asibiti a Kano.

An yi jana’izar sa da misalin ƙarfe 11:00 na safe a gidan sa da ke unguwar Goron Dutse, Kano.

‘Yan fim da mutanen gari sun halarci jana’izar, inda wurin ya cika maƙil babu masaka tsinke.

Wata majiya ta kusa da iyalin marigayin ta shaida wa mujallar Fim cewa daraktan, ɗan kimanin shekara 43, ya rasu ya bar mahaifiyar sa da matar sa da ‘ya’ya 15. A cikin ‘ya’yan, 11 ne nasa, huɗu kuma na wan sa da ya rasu ne, shi kuma ya ɗauko su ya haɗa su da ‘ya’yan sa.

Ana sallar jana’izar Nura Mustapha Waye

Labarin rasuwar Malam Nura ya kaɗa hantar mutane da dama, musamman ‘yan fim, ba kamar da yake mutuwar ta bazata ce.

Wasu ‘yan fim sun shaida wa mujallar Fim cewa ko a jiya-jiyan nan su na tare da daraktan, kuma babu alamar cewa ba shi da lafiya.

Babban furodusa kuma jarumin ‘Izzar So’, Lawan Ahmad, ya na daga cikin waɗanda su ka fara ba da sanarwar rasuwar, inda ya rubuta haka a Instagram: “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya karɓi rayuwar Nura Mustapha Waye, director Izzar So. Za a yi zana’idar shi ƙarfe 11 na safen nan a gidan sa Goron Dutse Primary in-sha Allah. Allah ya yafe masa kurakuran sa, amin. Allah ya sa idan tamu ta zo mu cika da imani, amin.”

Ali Nuhu kuma ya ce: “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya jarabce mu da babban rashi. Allah ya jiƙan ka Nura, ya kyautata makwanci. Allah ya sa Annabi ya karɓi baƙuncin ka. Jiya war haka mu na tare, ana ta raha. Allah ya jiƙan ka da rahama.”  

Sauran ‘yan fim maza da mata, babba da yaro, sun ci gaba da yi wa marigayin addu’ar samun rahama. Da yawan su sun wallafa hotunan sa da bidiyoyin sa inda ya ke bayyana shauƙin soyayyar sa ga Manzon Allah (s.a.w.).

Nura ya na sumbantar tuta mai ɗauke da sunan Manzon Allah (s.a.w.)

A soshiyal midiya a yau ko’ina ka leƙa maganar rasuwar Nura ake yi da kuma bayyana kyawawan halayen sa da irin soyayyar da ya ke yi wa Annabi Muhammadu (s.a.w.).

Allah ya rahamshe shi, amin.

Loading

Tags: Ali NuhudaraktaIzzar SoKannywoodKanoLawan AhmadmutuwaNura Mustapha Wayerasuwa
Previous Post

Furodusan Kannywood Murtala Aniya ya yi rashin ‘yar sa Fatieha

Next Post

Arafa: Mawaƙi Rarara na so masu hali su taimaki marasa galihu

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Rarara ya na gabatar da nasiha a cikin bidiyon

Arafa: Mawaƙi Rarara na so masu hali su taimaki marasa galihu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!