MASU harkar finafinan Hausa sun bayyana rasuwar babbar furodusa Hajiya Umma Ali a matsayin wani babban darasi ga kowannen su, musamman dangane da rashin makawar zuwan mutuwa a kowane lokaci.
Sun yi wannan nasiha ga juna ne a wajen babban taron yi wa marigayiyar addu’a a Kano a yau Lahadi, 8 ga Agusta, 2021, wato kwana bakwai da rasuwar babbar furodusar.
Hajiya Umma, wadda ita ce shugabar farko ta ƙungiyar mata masu ɗaukar nauyin shirya finafinan Hausa (furodusoshi), ta rasu ne a ranar Lahadi, 31 ga Yuli, 2021 a Asibitin Premier da ke Kano.
Majalisar Dattawan Kannywood (Kannywood Foundation), reshen Jihar Kano, ita ce ta shirya gangamin addu’ar wanda aka fara da misalin ƙarfe 4 na yamma a filin Social Welfare da ke Court Road, Gyaɗi-Gyaɗi.
Kafin a gabatar da addu’o’i na musamman, an yi nasihohi masu ratsa zuciya da sanyaya jiki daga bakin malamai da su ka haɗa da Malam Khalid Musa da Malam Ahmad Muƙaddas.
A jawabin sa, Malam Khalid ya ya bayyana cewa marigayiya Hajiya Umma Ali mutuniyar kirki ce kuma mai karamci tsakanin ta da abokan sana’ar ta da sauran al’umma.

Ya ce, “A duk lokacin da aka yi mutuwa, ɗan’adam ba ya buƙatar wa’azi saboda mutuwa ita ce wa’azi mafi girma ga mutane.
“Kwana ki goma da su ka shuɗe mu na zaune da Hajiya lafiya, ba wanda ya san cewa lokacin ta ya ƙarato na mutuwa. Idan ajalin mutum ya zo, to fa babu wani jinkiri, babu ragi, babu ƙari da za a yi wa wani ɗan’adam.”
Malamin ya ƙara da cewa, “Abu mafi muhimmanci da ya kamata mutane su sani kuma su na tambayar kan su a ko da yaushe shi ne wanne guzuri ka yi wanda zai zama abin da za ka girba a gobe ƙiyama? Ko mu na tunanin cewa idan mun mutu ba za a tashe mu ba? Ya kamata mu saka ɗan ba wajen ganin mun fuskanci ayyukan alheri.
“Alhamdu lillah! Ayyukan alheri shi ne guzurin Hajiya Umma Ali, domin kuwa shi ne ma wanda ya tara mu a nan. Kyawawan ɗabi’un ta nagari da kuma taimakon ta da ta ke yi wanda ba ta neman yabon wanda ta yi wa ko godiya, wannan kuma duk wanda ya san ta zai gaya maka haka a cikin ɗabi’un ta nagari.
“A cikin mutane goma da na sani a rayuwa ta wanda za a ce na lissafo domin karamcin su, to wallahi Hajiya ta na daga cikin na farko-farko.”
Ya kuma bayyana yin aiki nagari a matsayin wanda a ko da yaushe mutane za su riƙa tunawa da kai ko da bayan rayuwa.

Malam Khalid ya ƙarƙare nasihar tasa da jan hankali ga iyalan marigayiya da su ci gaba da haɗa kai domin su ɗora kan ayyukan alherin da ta bari.
Shi ma Malam Ahmad Muƙaddas, a jawabin sa, ya bayyana marigayiyar a matsayin wata jajirtacciyar mace wadda Kannywood ba za ta taɓa mantawa da irin gudunmawar da ta bayar ga masana’anar ta ba matuƙar harkar ta na nan ana ci gaba da tafiya.
Ya bayyana mutuwa a matsayin wata aba da ke sauya wa mutum zango. Ya ce: “Mutuwa wata aba ce da ta ke sauya wa mutum zango. Ka zo ne ka koma. Akwai waɗanda ana musu sauka lafiya idan ka mutu, akwai kuma wanda ake Allah-Allah a binne ka.
“Mutuwa wa’azi ce. Da ba a mutuwa da ba a ɗauki Ma’aikin Allah ba da sauran manzanni da salihan bayi.”
Bugu da ƙari, ya ce, “Allah ya yi alƙawari ga duk waɗanda su ka yi aiki na alkairi sakamakon mutum shi ne Aljanna. Abin da zai hana mutum shiga Aljanna shi ne sai dai idan ɗan’adam bai mutu ba.
“Ba wai mutum ya mutu shi ne abin jin ba, me ka bari na alkairi kamar sadaƙa mai gudana, ‘ya’ya nagari da sauran ayyukan alkairi.”
A ƙarshe, ya rufe jawabin da cewa, “Hajiya ta amfanar da mu, ta taimaka wa tafiyar Kannywood. Matuƙar za a wayi gari ana ci gaba da musuluntar da harkar masana’anatar Kannywood, to fa ba za a manta da ayyukan ta nagari ba da ta yi. Allah ya yi mata rahama.”

Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, babbar aminiyar marigayiya Hajiya Umma Ali, ita ma ta yi jawabi inda ta bayyana marigayiyar a matsayin mace mai zumunci a tsakanin ta da ‘yan’uwan ta da mutanen da su ke cikin wannan masana’anta.
Ta ce, “Abu guda da zan iya faɗa kuma wanda aka manta ba a faɗa ba shi ne Hajiya Umma ta na da zumunci, zumuncin da duk wani ɗan’uwan ta ya yi kuka da rashin ta.
“Ba iya iyalan ta da ‘yan’uwan ta ne kawai su ka yi asara da rasuwar ta ba, har mu da mu ke wannan masana’anta. Babu wani gida da ake shiga a yi dabdala a cikin wannan masana’anatar irin gidan ta. Ta riƙe kowa da kowa a matsayin ‘ya ‘yan ta!”
Da faɗin haka, Hajiya Balaraba sai kuka.
Shi ma a nasa bayanin, shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya bayyana cewa marigayiyar mutuniyar kirki ce. Ya ce, “Kowa shaida ne Hajiya mutuniyar kirki ce.
“Kada mu manta kowa zai koma ga Allah. Mutuwa ƙofa ce, kowa da mu ke gani sai ya bi ta wannan ƙofar. Mu yi aiki nagari domin kyakkyawan gobe.”
Afakallah ya ƙarƙare da yin kira ga iyalan marigayiyar da su yi ƙoƙari su kwatanta abin da ta yi lokacin rayuwar ta.

Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Dakta Ahmad M. Sarari, ya bayyana marigayiyar a matsayin mutuniyar kirki tare da yi mata addu’ar samun tsira da falalar Allah.
Bayan kammala dukkan nasihohi da jawaban wasu daga cikin manyan baƙi, an gudanar da addu’o’i na musamman domin neman gafara da rahama ga marigayiya Umma Ali.
Dandazon al’umma ne su ka halarci gangamin addu’o’in waɗanda su ka haɗa da ‘yan’uwa da abokan arzikin marigayiyar.
Kaɗan daga cikin ‘yan fim da marubuta da mujallar Fim ta gani su ne: Ado Ahmad Gidan Dabino, Shu’aibu Yawale, Alhaji Auwalu I. Marshal, Ahmad S. Alkanawy, Falalu A. Ɗorayi, Kabiru Maikaba, Abdullahi Zakari, Sani Indomie, Ishaq Sidi Ishaq, Alhassan Kwalle, Ɗan’azimi Baba Ceɗiyar ‘Yangurasa, Bala Anas Babinlata, Shehu Bello, Aliyu Sambo, Maryam Mohammed Ɗanfulani (Mashahama), Mu’azzam Boss, Rashida Adamu Abdullahi (Maisa’a), Maryam Booth, Maryam Dodo, Hauwa A. Bello (Edita), da sauran su.




