• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 2, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rawar da ƙungiyoyin YBN da 13×13 ke takawa a siyasar Kannywood

by DAGA ABBA MUHAMMAD
March 7, 2022
in Nijeriya
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A CIKIN ‘yan kwanakin nan an samu rabuwar kai a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, tun bayan ɓullar wata ƙungiyar mai suna ’13×13 Awareness Group’. Fitaccen mawaƙin siyasa  Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) shi ne jagoran ƙungiyar.

Kafin a kafa ƙungiyar, akwai wata ƙungiyar mai suna YBN (wato Yahaya Bello Network), wadda aka ƙaddamar da a shekarar da ta gabata. Ita YBN, fitaccen furodusa Abdul Amart Mohammed (Maikwashewa) ne ya kafa ta don yin kira ga Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Adoza Bello, da ya amince ya fito takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai gabatowa a 2023. A yanzu haka haƙar su ta cimma ruwa, domin gwamnan ya amsa kiran nasu.

A YBN akwai wasu daga cikin mawaƙa, daraktoci, furodusoshi da jaruman Kannywood waɗanda su ka kasance jakadun ƙungiyar, kuma su na tare da Abdul Amart lokacin da su ka yi waƙar ‘Sakamakon Canji’, duk da cewa akwai wasu daga cikin mawaƙan da su ka bar tafiyar tun bayan zaɓen 2019, wasu kuma a yanzu sun samu shiga.

Haka ita ma 13×13 ta haɗa da fitattun manyan fasihan mawaƙa, waɗanda su ne ƙashin bayan tafiyar ƙungiyar, sannan akwai fitattun daraktoci, furodusoshi da kuma ‘yan wasa da sauran su a cikin ƙungiyar.

Haƙiƙa YBN ta samu karɓuwa a wurin al’umma na ciki da wajen Kannywood, kuma da ma an ƙirƙire ta ne don siyasar Yahaya Bello, saboda haka a lokacin ƙaddamar da ita, bayan shugaban ta na ƙasa, sai kuma aka tsinka ta gida 19, wanda a dukkan jihohin a Arewa 19 ta na da ciyaman da kuma membobi. 

Sanadiyyar ƙungiyar, ‘yan Kannywood da dama sun mallaki motoci, kuɗi da sauran abubuwa daga wurin Abdul Amart.

To, abin da mutane da dama ba su fahimta ba shi ne ’13×13 Awareness Group’ da ‘Yahaya Bello Network Group’ abu ne guda biyu ba ɗaya ba. Dalili kuwa, abu na farko  an kafa 13×13 ne don manufofi da dama, ba don siyasa kawai ba, kamar yadda jagororin tafiyar su ka bayyana manufofin ƙungiyar. Daga ciki akwai wayar da kan al’umma, taimakon juna da kuma al’umma, haka kuma idan tafiyar siyasa ta zo za su dubi ‘yan takarar da su ka cancanta su yi masu aiki.

Jagoran YBN, Abdul Amart Mohammed

Abu na biyu, 13×13 ta ɓangaren siyasa ba ta tsaya a kan mutum ɗaya ba, domin idan aka yi la’akari da irin yadda tawagar ƙungiyar ke ziyartar manyan ‘yan siyasar ƙasar nan tun bayan kafa ta, za a gane cewa da bambanci a tsakanin ta da YBN, kuma abubuwan da su ka bambanta su da dama.

Amma kuma 13×13 da YBN ta wani ɓangaren kuma abu ɗaya ne, domin dukkan su a ƙarƙashin Kannywood su ke; dukkan su daga daraktoci, furodusoshi, ‘yan wasa, mawaƙa da sauran ke cikin tafiyar babu wani wanda ba ɗan Kannywood ba ne.

Haka kuma su na yin abubuwa kusan ɗaya ta wani ɓangaren. Dukkan su kafin a kafa su, shugabannin su na ƙoƙarin tallafa wa abokan sana’ar su marasa ƙarfi. A bara, Rarara ya bada kyautar kuɗi N50,000 kowanen su ga dattijan Kannywood aƙalla mutum 60. A karo na biyu, ya bada kyautar motoci da gidaje ga mutane da dama. 

Shi ma Abdul Amart ya riƙa yin ire-iren waɗannan kyaututtukan. 

Ana iya cewa kusan su biyun ne ke riƙe da Kannywood a yanzu. ‘Yan fim da dama a ƙarƙashin su su ke ci da sha, har ma su ma su taimaki wasu.

Don haka ba abin mamaki ba ne don yau su na jagorantar ƙungiyoyi, sun yi abubawa da dama, kuma baya sun saba yi.

Da kafuwar 13×13 ba a kai wata biyu ba cikakku, amma ta yi abubuwan da za a yaba mata. A kwanan baya ta ziyarci wani gidan marayu a Kano, inda ta kai masu tallafin kayan abinci mai tarin yawa. Haka kuma ta ziyarci gidan yari a Kano, ta fitar da masu ƙananan laifuka. Haka ta yi a Sokoto, inda ta fitar da masu ƙananan laifi 33 daga kurkuku tare da ba su jari. Waɗannan abubuwa da ƙungiyar ta yi su na daga cikin manufofin ta.

A watan jiya, YBN ta tallafa wa iyalan ‘yan Kannywood da su ka rasu da kuma waɗanda ke cikin halin rashin lafiya da kuma waɗanda girma ya kama su da kuɗaɗe.

Amma kuma duk da irin waɗannan bambance-bambance da ke tsakanin su, akwai wasu ‘yan fim da ke neman haddasa rikici a tsakanin su, har ana yi wa juna kallon hadarin kaji.

Wasu na faɗin cewa ai Rarara ya kafa 13×13 ne domin karya Abdul Amart da ƙungiyar sa ta YBN. Wannan maganar daga bakin wasu daga cikin ‘yan Kannywood ta ke fitowa, don ba a ji maganar daga bakin wani ɗan 13×13 ko ɗan YBN ba. A haka har an samu wasu daga cikin masoyan  ƙungiyoyin biyu su na ta yin habaice-habaice a soshiyal midiya, wanda har ta kai ga fitaccen darakta Falalu A. Ɗorayi ya yi rubutu mai jan hankali game da ƙungiyoyin biyu mai taken “Tsakanin YBN da 13×13” a cikin irin rubuce-rubucen da ya ke yi na goron Juma’a.

A rubutun nasa, daraktan ya ce, “A mahanga ta, duk ƙungiyoyin su na aiki ne kusan iri ɗaya, taimakon mutanen masana’antar da mutanen wajen ta. Wannan abu ne da idanu su ka gani su ka tabbatar.”

Ɗorayi ya cigaba da cewa, “Shawara ce domin masalaha. Kar ku ba wa shaiɗan dama wajen shiga tsakanin ku, kuma kar ku ba wa zuciya dama ta jefa muku gaba ko ƙiyayya. Ku yi komai domin Allah. Kar ku bada gurbin habaici tsakanin ku. Ku nuna dattaku ku cigaba da samar da alkhairi da yaɗa shi a tsakanin mabuƙata. Wannan ɗabi’a ce tagari.

“Abin alfahari, Kannywood ta haɗa ku cikin sana’a da nema. Kafin zuwan ƙungiyoyin, abokan juna ne ku, sana’ar ku ɗaya, wurin zaman ku ɗaya, ku na kwana wuri ɗaya tare, kun ci abinci tare a kwano ɗaya. Hakan ya na nuni da ƙauna, zumunci da abokantaka.

“Duk wata alfarma da arziƙi da ya ke tare damu mun same shi sanadin Kannywood. Me zai hana ku maida hankali wajen godiya ga Allah da ci-gaba da taimakon da ku ka saba, maimakon ƙoƙarin ba wa Shaiɗan dama ya haifar da gaba.

“Da ƙaunar juna mu ka zo duk inda mu ke, da ƙaunar juna ne za mu wuce inda mu ke a yanzu.

Ina roƙon jagororin ƙungiyoyin, ina gama ku da Allah da Annabi, ku yi duba da alkhairin da ku ke rabawa da farin ciki da su ke sakawa a zukata masu yawa, ku yi aiki da hankali kar ku bari Shaiɗan ya haifar da gaba da habaici tsakanin ku.”

Falalu Ɗorayi ya kawo wani Hadisi, inda ya ce, “Abu Hurairah ya ce, Rasulillahi (S.A.W) ya ce, ‘Ba za ku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, ba za ku yi imani ba har sai ku na son junan ku. Shin ku na son in yi muku nuni da abin da idan ku ka aikata shi za ku so junan ku? Ku yaɗa sallama a tsakanin ku” (Muslim: 54).”

Dauda Rarara, jagoran 13×13

Wannan jan hankali na Falalu ya yi wa mutane da dama daɗi, domin ya yi amfani da hikima wurin isar da saƙo ga jagororin ƙungiyoyin, kuma saƙon ya isa gare su, tunda babu wanda bai gani ba a cikin su.

To, wannan kenan. YBN da 13×13 dai ƙungiyoyi ne mabambanta. Sai dai ayyukan alkhairan su ne ya zo kusan ɗaya.

Kuma har yanzu ita 13×13 ba ta fara yaɗa wata manufa ta siyasa ba, saɓanin YBN da ta ke yi don siyasa, domin siyasar ce ƙashin bayan ƙungiyar. Kuma idan aka yi duba da sunayen ƙungiyoyin, wannan ya ishi mutane tantance tsakanin su.

Yanzu al’umma da kuma sauran jama’ar Kannywood ya kamata su yi alƙalanci a kan wannan lamari. Sannan su yi alƙalanci a kan masu cewa an ƙirƙiri 13×13 ne don a karya Abdul Amart da YBN.

Loading

Tags: 13×13 Awareness GroupAbdul Amart Mohammed Maikwashewababban zaɓen 2023Dauda Adamu Abdullahi KahutuFalalu A. DorayiKannywoodKogikurkukuRararaSakamakon CanjisiyasaYahaya Adoza BelloYahaya Bello NetworkYBN
Previous Post

Abin da ya sa ban aurar da ‘ya ta ba kamar yadda na yi niyya – Rikadawa

Next Post

Yadda ‘ya’ya na 4 su ka rasu a hɗarin mota, aka ce wai har da ni – Jarumin Kannywood Balarabe Jaji

Related Posts

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Ɗangote sun halarci jana’izar Aminu Ɗantata a Saudiyya

July 1, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina

June 30, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

June 23, 2025
Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya
Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya

June 21, 2025
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu
Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu

June 20, 2025
Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Next Post
Alhaji Balarabe Jaji

Yadda 'ya'ya na 4 su ka rasu a hɗarin mota, aka ce wai har da ni - Jarumin Kannywood Balarabe Jaji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!